HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WADDA YA YI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARAFAT KENAN).

 

 

HUDUBAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM WADDA YA YI A KHUDUBAR RANAR TARA GA WATAN ZUL-HIJJAH, SHEKARA TA GOMA DA HIJIRA A DUTSEN ARAFAT (RANAR ARAFAT KENAN).

 

 

ANNABI (SAW) YA FARA DA CEWA:

“Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a wannan wuri a yau.

Ya ku mutane kamar yadda ku ka riki wannan wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa mutane kayan da suka ba ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku. Ku tuna fa, hakika Allah zai yi sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi.

 

Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.

 

Ya ku jama'a hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma su ma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su, Kuma ku tufatar da su akan jin kai. ku bi da su kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu domin su majibintan al'amurran ku ne, kuma mataimakan ku, Hakki ne akan su da kar su yi abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci zina.

 

Ya ku jama'a, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah(SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, Ku azumci watan Ramadan, kuma ku bada zakka. Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi. Ku sani fa, kowane musulmi dan'uwan musulmi ne. Dukkan ku daidai ku ke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da aikata kyawawan ayyukka.

 

Ku tuna fa (ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban Ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku, saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.

Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka ku yi tunani sosai akan wannan magana da na gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).

 

Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); (Alkur ani) ga kuma (Sunnah). Idan kun bi wannan ba za ku taba bata ba. Duk wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, su ma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji magana daga karshe su fi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.

Ya Allah ka zamo shaida a gare ni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.”

 

'Yan uwa ku yada wannan KHUDUBAR ga 'yan uwa musulmi wanda kamar yau aka yi ta!!!

 

 

 

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA