BAYANIN KADAN AKAN ALJANNAH
BAYANIN KADAN AKAN ALJANNAH An gina Aljannah ne da tubali (blocks) na Zinare da Azurfa tatacciya. Simintin cikinta anyi shine da Almiski mai mutukar Qamshi. An cike tsakanin tubalanta da kayan ado na Zubarjadi da Yaaqootu. An halicci Qasar cikinta ne daga Za'afaran. Tana da Qofofi guda takwas kamar haka: 1. Jannatul Ma'awa. 2. Daarul Maqaam. 3. Daarus Salaam. 4. Daarul Khuld. 5. Jannatul 'Adni. 6. Jannatun Na'eem. 7. Jannatul Khaseef. 8. Jannatul Firdaus. • JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa, • JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya • JANNATUL FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa. Acikin Aljannah akwai Gonakai da lambuna wanda tsawon kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara 100 ko fiye da haka. Akwai bishiyoyi masu inuwa masu Ni'ima da tsirrai marassa Qaya. An Halicci bishiyoyim cikinta ne daga madaukakin Zinare da tatacciyar Azurfa. Suna da manyan ganye kamar girman kunnen giwa, kuma 'y...