BAYANIN KADAN AKAN ALJANNAH
BAYANIN KADAN AKAN ALJANNAH
An gina Aljannah ne da tubali
(blocks) na Zinare da Azurfa tatacciya. Simintin cikinta anyi shine da Almiski
mai mutukar Qamshi.
An cike tsakanin tubalanta da
kayan ado na Zubarjadi da Yaaqootu.
An halicci Qasar cikinta ne
daga Za'afaran.
Tana da Qofofi guda takwas
kamar haka:
1. Jannatul Ma'awa.
2. Daarul Maqaam.
3. Daarus Salaam.
4. Daarul Khuld.
5. Jannatul 'Adni.
6. Jannatun Na'eem.
7. Jannatul Khaseef.
8. Jannatul Firdaus.
•JANNATUL MA'AWA ita ce daga Qasa,
•JANNATUL ADNI kuma ita ce matsakaiciya
•JANNATUL
FIRDAUSI kuma ita ce Qololuwa.
Acikin Aljannah akwai Gonakai
da lambuna wanda tsawon kowacce gona da fadinta ya kai tsawon tafiyar shekara
100 ko fiye da haka.
Akwai bishiyoyi masu inuwa
masu Ni'ima da tsirrai marassa Qaya.
An Halicci bishiyoyim cikinta
ne daga madaukakin Zinare da tatacciyar Azurfa.
Suna da manyan ganye kamar
girman kunnen giwa, kuma 'ya'yan itacen bassu Qarewa. Suna nan nau'i-nau'i.
Wadanda suke Qaunar juna
domin Allah zasu samu shiga Aljannah kuma acikinta za'a basu wasu Al'amudai na
Yaqootu.
Akan Al'amudan akwai Dakuna
(rooms) guda dubu saba'in (70,000) masu haske.
Kuma hasken Wadannan dakunan
ne zai haske 'Yan Aljannah kamar yadda hasken rana yake haske mutanen duniya.
Akwai dakunan cin abinci yalwatattu
ta yadda acikin dakin cin abinci guda za'a samu shimfidu (dining sheet) guda
dubu saba'in (70,00).
Akwai Qananan yara masu hidima,
suna zagayawa ko ina cikin gidan Aljannah. Sunci ado da kaya iri-iri. Kuma Su
kansu suna haske kamar Lu'u-Lu’u.
Bishiyoyin dabinai da inabi
wadanda 'ya'yansu ko yaushe nunannu suke. Kuma suna daf da Qasa. Girman kowanne
nonon dabino yakai kamar Zira'i 12.
Kuma kowanne kwayan dabino
guda ya kai girman Tulu, Kuma fari ne tas kamar madara, Kuma babu Kwallo acikinsa.
Zakinsa kuma wane Zuma!!
Kuma girman kowanne Inabi
guda daya yakai girman tulu.
Sai wani Sahabi yace "Ya
Rasulallahi guda daya zai isheni dani da iyalaina?"
Sai ANNABI (S.A.W) yace masa "AI
GUDA DAYA ZAI ISHEKA
DAKAI DA KABILARKA MA BAKI DAYA"
TUFAFIN 'YAN ALJANNAH:
Kowanne Dan Aljannah za'a
sanya masa riguna guda 70 na haske. Masu taushi, masu kyalli, Kuma marassa
nauyi ko kadan.
Wadannan rigunan kowacce
kalarta daban, nau'inta daban. Kuma ba irin tufafin duniya bane, domin kuwa
babu wacce take rufe 'yar uwarta.
Saboda tsananin haskensu da
kyawunsu, ana iya ganin Siffar jikin mutum har Zuciyarsa da irin Qarfin
soyayyar da take dauke dashi.
Wadannan Tufafin bassu tsufa
ko datti, kuma bassu yagewa.
QORAMUN ALJANNAH
Acikin Aljannah akwai Qoramu
(Kogi) guda bakwai:
1. Kogin ruwa.
2. Kogin Madara.
3. Kogin ruwan Zuma .
4. Kogin ruwan giya (Sharabun
Tahoorun).
5. Kogin Kafoor.
6. Kogin Zanjabeel.
7. Kogin Tasneem.
Ya Allah muna tawassuli da
fiyayyen bawonka wato ANNABI (S.A.W) domin alfarmarsa ka gafarta mana kasa muna
cikin 'Yan Sahun gaba wajen shiga Aljannah Albarkan ANNABI S.A.W.
Comments
Post a Comment