FALALAR KARANTA ALQUR’ANI MAI GIRMA
FALALAR KARANTA ALQUR’ANI MAI GIRMA
1- Hakika babu kokonto karatun Alqurani
yana daga cikin mafifitan ayyuka sannan kuma yana daga cikin mafi girman abinda
bawa zai nemi kusanci dashi zuwa ga ubangijinsa mai girma da daukaka.
An sharanta ga ko wane mumini da
mumina da suyawaita karatun Alqurani mai girma ga namiji da mace babba da yaro
an sharanta ga kowa da kowa dasu yawaita karantashi, saboda abinda ke cikinsa
na alkairi mai girma da faida mai yawa kamar yadda Allah mai girma yace : HAKIKA WANNAN ALQURANI YANA SHIRYAWA ZUWA
GA HANYA MAFI TSAYUWA KUMA YANA YIWA MUMINAI BUSHARA WADANDA SUKE YIN AIKI NA
KWARAI HAKIKA SUNADA LADA MAI GIRMA: ALISRAU
2- ALLAHU (SHN) yana cewa: KACESHI
WANNAN ALQURANI SHIRIYANE KUMA WARAKANE GA WADANDA SUKAYI IMANI. FUSSULAT:44.
3- Allahu madaukakin sarki yace inda
yake yabon masu karanta Alqurani: HAKIKA WADANDA SUKE KARANTA LITTAFIN ALLAH
SUKA TSAIDA SALLAH SUKA CIYAR DAGA ABINDA MUKA AZURTASU A FILI KO A BOYE SUNA
KAUNAR KASUWANCI WANDA BABU HALAKA A CIKINSA. FADIR: 29
4- MANZON ALLAH (S.A.W) yace: Kukaranta
ayar Alqur’ani hakika zaizo ranar alkiyama yana mai ceton masu karantashi.
5- Mai tsira da amincin Allah yace: mafi
alkairin ku wanda ya karanta Al’qur’ani kuma ya karantar dashi.
6- Manzon Allah yace: wanda yana tare da
manyan mala’iku masu girma, wanda yake karanta Alqur’ani yake shan wahalar
karantashi yana mai tsanani agareshi yana da lada biyu.
7- Ko wanda harafin da musulmi ya
karantashi daga cikin Al’qur’ani yana da lada, saboda karatun Alqur’ani yana
shagaltar da mutum ga barin yi da mutune da annaminaci, Manzon Allah yace:
wanda ya karanta harafi daga littafin Allah yanada ladan kyakykyawan aiki kuma
kyakykyawan aiki yanada lada misalin goma. Ba ina cewa alif lamin harafi. A’a
alif harafine, lam harafine, min harafine.
8- Manzon Allah ya kasance wata rana
azaune acikin sahabbansa yace: wanene daga cikinku zaiso ya fita zuwa (Badaha)
yadawo da taguwa biyu manya batare da
zunubi ba, ko yanke zumunta? Sai suka ce muna son haka. Yace: dayanku yaje
masallaci ya nemi sanin aya daya yafi abashi taguwa uku, ayoyi hudu sunfi masa
taguwa hudu da kwatankwacin adadinsu na rakuma.
9- Manzon Allah (S.A.W) yace: misalin
mumininda yake karanta Alqur’ani kamar lemon tanjirin ne kamshinsa mai dadi
dandanosa mai dadi, misalin muminin da baya karanta Alqur’ani kamar dabino
bashi da kamshi dandanonsa mai zaki, misalin munafikin dayake karanta Alqur’ani
kamar tazargade ce mai dadin dandanonta mai daci, misalin munafiki baya karanta
Alqur’ani kamar gunace batada kamshi dandanonta mai daci.
10- Abusa Zaburar
wa ga karanta Alqur’ani mai girma yakamata ga abokai da tsaraiku su dinga taruwa dan karantashi da yin darasunsa
saboda falala mai girma dake cikin yin hakan, Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:
mutane basu taruba aikin daki daga dakunan Allah face sun karanta littafin
Allah Sunayin darasunsa a tsakaninsu face sai nutsuwa ta sauka a garesu kuma
rahama ta lullubesu kuma mala’iku sun kewayesu kuma Allah ya ambacesu acikin wanda suke wurusa. Sune
(Mala’iku)
don duba ko download na qura'ani mai fasarar Hasusa <a href="http://fm.nextwapblog.com/79556">Latsa nan</a>
don duba ko download na qura'ani mai fasarar Hasusa <a href="http://fm.nextwapblog.com/79556">Latsa nan</a>
Allah ya ƙarama na sonshi
ReplyDelete