KAIKAYI YA KOMA KAN MASHEKIYA

Wata mata ce ta samo guba don ta sawa mijinta a

abinci ya mutu taci gadonsa.

sai ta barbada guban a miyar da mijin zai ci, bayan

ta gama juya gubar a miyar maigida sai ta manta

ta tsotse yatsar data juya miyar dashi saboda saba

tsotse yatsa a miya da tayi ai take sai ta hau shure- shure cikinta na murdawa.

tana cikin Ihu sai maigida ya shigo ya kwasheta

zuwa asibiti aka kaita emergency.

maigida ya ruga gida dauko kudin asibiti sai ya

tarad yaransa a qasa suna ta birgima suna ihu

cikinsu ya murde, ashe sun dawo makaranta suna

jin yunwa sai suka ci abincin babansu don yakan

basu damar su dinga daukar abincinsa suci ko

baya nan idan suna jin yunwa sun dawo
makaranta.

haka ya kwashesu su biyu a mota zuwa asibiti aka

hada da mamansu akayi treatment dinsu duk suka

sami lafiya inda likita ya gano guba suka ci a

abincin, wanda hakan tasa aka gane matar ce tasa

gubar don ta kashe mijinta shine ya koma mata,

don dai akan abin duniya kawai mai qarewa.

anan ta nemi afuwar mijinta ya yafe mata sannan

ta gyara halayenta ta zama saliha matar kirki.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA