Posts

Featured Post

Labarin Wata Mata Mai Aikin Gidan Nama

Image
LABARIN WATA MATA MAI AIKIN NAMA Takansance tana  aiki a wata masana'antar saida nama ga masu bukata.  Wata rana bayan tazo wurin aikinta ta kuma kamala aikin, Sai ta tafi dakin sanyi wato inda ake ajiya naman da ba'a sayarba (meats Cold freezer) don yin bincike akai.  Shigar dakin nata ke da wuya sai kofar dakin sanyin ta rufe Ruf.  Tayi - tayi ya bude amma ina kofa taQi budewa tayi bugu iya bugun kofar ko Allah zaisa wani yajita ya kawo mata dauki amma ina babu wada yaji.  Tayi kuka iya kuka amma ina babu wanda yajita, kuma sanyin dakin yafi karfin dan adam ya iya jure shi zuwa wani lokaci.  Gabadaya ma aikatan masana'antar suntafi maana sun tashi a aiki.  Bayan kamar awanni 5 Tana daf da mutuwa a cikin dakin sanyi , katsam sai mai gadin masana'antar ya bude kofar.  Bayan ta dawo daga hankalinta, sai take tambayar  mai gadin Tayaya har kazo ka bude wannan kofar bayan baka ...

DAREN LAILATUL-QADAR

Image
Daren LAILATUL QADR ya fi watanni dubu wanda ba wannan daren a cikinsa alheri, haka Qur’ani ya bayyana alherinsa ya fi na shekara tamanin da wata hudu. Hadisai sun zo suna bayanin samun wannan dare a cikin watan Ramadana ne. Sunna ta tabbatar kamar yadda Allah ya ce; • Kuma ana samunsa a cikin goman karshen Ramadan. • Ana samun wannan dare ne a cikin kwanukan mara, kamar daren 21,23,25,27,29, • Amma an fi sa ran samunsa a daren ashirin da bakwai (wato bayan an kai azumi na ashirin da shida). Amma hadisi ya zo MANZON ALLAH ( Salallahu Alaihi Wasallam ) yace “ku neme shi (daren lailatul qadr) a dare na mara”. An so mutum ya dage da ibada a cikin wannan daren ya raya sa da nau’o’in ibada, kamar karatun Alkur’ani da nafila da zikiri, hakanan ma an so mutum ya umurci iyalinsa da yin ibada a daren su dukkansu. • MANZON ALLAH (S alallahu Alaihi Wasallam)  ya ce wanda ya yi tsayuwar daren lailatul qadri Allah ya gafarta masa zunubansa wadanda suka gabata. ...

GA WASU HADISAN ANNABI S A W MASU MATUKAR MUHIMMANCI

*Mai yakai Hadisan Annibi Dadi?*  * HADISI NA FARKO *  Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi masa Alkawarin zai gina masa katafaren gida a gidan Aljanna. Sai Sayyidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawaitawa, sai Manzon Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah shine mai tsabtacewa.  * HADISI NA BIYU *  Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata jumaa mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki. * HADISI NA UKU *  Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce duk wanda ya haddace ayoyin goma na farkon kahfi Allah zai kiyaye shi daga fitinar Dujjal.  * HADISI NA HUDU *  Manzon Allah yana cewa Wanda ya karanta ayatul kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba.  * HADISI NA BIYAR *  Idan kazo zaka kwanta a shimfidar ka da daddare...

Farillan Alwala

Image
.                *FARILLAN ALWALA* Farillan alwala guda 7 neh: • Niyya • Wanke Fuska • Wanke hannaye zuwa gwiwar hannu • Shafar kai • Wanke kafafuwa • Cuccudawa • Gaggautawa                   *SUNNONIN ALWALA* • Wanke hannaye zuwa wuyan hannu • Kurkure baki • Shaka ruwa • Fyacewa • Juyo da shafar kai • Shafar kunnuwa • Sabunta ruwa agaresu • Jeranta tsakanin farillah              *MUSTAHABBAN ALWALA* • Yin bismillah • Goga asuwaki • Kari akan wankewa ta farko a fuska da hannaye • Farawa daga goshi • Jeranta sunnoni • Qaranta ruwa a nisa gabobi • Gabatar da dama kafin hau.               *AKAN FASALIN ALWALA* • Wanda ya manta da wata farilla daga gabobinsa, idan ya tuno sai ya aikata ta da abunda ke bayanta, idan kuma yayi nisa sai ya aikata ta ita kadai, ya kuma sake abunda ya sallata bayan faruwa...

HANYOYI DON MAGANCE CIWON HANTA hepatitis

Image
Ciwon hanta na daya daga cikin manyan ciwuka da suke da wuyar magancewa a duniya amma da Yardar Allah duk Wanda yabi abun da zamu fadi za’a samu waraka da Yardan Allah. ALAMUN CIWON HANTA Akwai matsanancin ciwon kai da ciwon malariya da typhoid akai-akai, Haka zakaji ciwon jiki da rashin karfin jiki, ciwon ciki mai tsanani, Yawan haraswa dakuma tashin zuciya koda ruwa kasha, Ido yakanyi yellow, da rashin dandano a baki, fitsari ya koma yellow, ko matsananci zazzabi da jin sanyi ,bayan gidan mutum yakan koma kalan kasa. Ga duk Wanda yaji wadannan alamu sai yayi kokarin zuwa asibiti domin Gwaji A daina tsoron gwaji domin magance cutar tana farkonta yafi sauki akan sanda zata tsananta. Masu ulcer dake yawan ciwon ciki da yawan haraswa da tashin zuciya suna magani ba sujin sauki suyi kokarin duba lafiyar hantar su domin takan hadu da masu ulcer sosai. MAGANINTA 1. A samu garin habba cokali 10 2. Garin Sidir cokali 5 3. Garin tin cokali 5 4. Garin bawon kankana...

JERIN SUNAYEN SARAKUNAN KANO.

Image
JERIN SUNAYEN SARAKUNAN KANO . 1. Bagauda 999-1063 2. Warisi 1063-1095 3. Gajimasu 1095-1134 4. Nawata & Gawata 1134-1134 5. Yusa 1136-1194 6. Naguji 1194-1247 7. Guguwa 1247-1290 8. Shekarau 1 1290-1307 9. Tsamiya 1307-1343 10. Usman Zamna Gawa 1334-1349 11. Yaji 1 (Ali) 1349-1385 12. Bugaiya 1385-1390 13. Kanajeji Dan Yaji 1390-1410 14. Umaru 1410-1421 15. Dauda 1 1421-1438 16. Abdullahi Burja 1438-1452 17. Dakuta 1452 18. Atume 1452 19. Yakubu Dan Abdullahi 1452-1463 20. Muhammadu Rumfa 1463-1499 21. Abdullahi 1499-1509 22. Muhammadu Kisoke 1509-1565 23. Yakubu 1565 24. Dauda Abasama 1565 25. Abubakar Kado 1565-1573 26. Muhammadu Shashere 1573-1582 27. Muhammadu Zaki 1582-1618 28. Muhammadu Na Zaki 1618-1623 29. Muhammadu Alwali 1 El kutumbi 1623-1648 30. Alhjai Dan Kurumbi 1648-1649 31. Shekarau 11 1649-1651 32. Kukuna Dan Alhaji 1651-1652 33. Soyaki 1652 34. Kukuna 1652-1660 35. Bawa Dan Kukuna 1660-1670 36. Dadi Dan Bawa 1670-1703 37...

Rahama Sadau, Jarumar wasan Hausa, ta sha da kyar a hannun dalibai masoyanta

Image
Rahama Sadau, Jarumar wasan Hausa, ta sha da kyar a hannun dalibai masoyanta Lamarin ya faru ne a jami'ar Umaru Musa dake Jihar Katsina Jami'an tsaron jami'ar sun yi nasarar tserar da ita ba tare da samun lahani ba Rahama Sadau, Shahararriyar jarumar wasan Hausa, ta sha da kyar a hannun wasu masoyanta, daliban jami'ar Umaru Musa dake jihar Katsina. Tun farko shugabannin kungiyar daliban jami'ar ne suka gayyaci jarumar domin karramata a bikin ranar Mata ta duniya. Saidai lamarin ya kwacube bayan isowar jarumar harabar taron, Students Centre, dake cikin jami'ar. Majiyar mu ta bayyana mana cewar jarumar ta iso wurin taron a makare, kuma zamanta keda wuya a teburin manyan baki sai dalibai suka barke da sowa da murnar ganin ta. Dalibai da dama sun nufi jarumar domin samun damar daukan hoto tare da ita, lamarin da ya kai an kasa sarrafa dandazon matasa masoya ga jarumar dake son yin hoton da ita. Rahoton da muka samu ya tab...