DAREN LAILATUL-QADAR




Daren LAILATUL QADR ya fi watanni dubu wanda ba wannan daren a cikinsa alheri, haka Qur’ani ya bayyana alherinsa ya fi na shekara tamanin da wata hudu.



Hadisai sun zo suna bayanin samun wannan dare a cikin watan Ramadana ne. Sunna ta tabbatar kamar yadda Allah ya ce;


• Kuma ana samunsa a cikin goman karshen Ramadan.


• Ana samun wannan dare ne a cikin kwanukan mara, kamar daren 21,23,25,27,29,


• Amma an fi sa ran samunsa a daren ashirin da bakwai (wato bayan an kai azumi na ashirin da shida).


Amma hadisi ya zo MANZON ALLAH ( Salallahu Alaihi Wasallam ) yace “ku neme shi (daren

lailatul qadr) a dare na mara”.


An so mutum ya dage da ibada a cikin wannan daren ya raya sa da nau’o’in ibada, kamar karatun Alkur’ani da nafila da zikiri, hakanan ma an so mutum ya umurci iyalinsa da yin ibada a daren su dukkansu.


• MANZON ALLAH (S alallahu Alaihi Wasallam)  ya ce wanda ya yi tsayuwar daren lailatul qadri Allah ya

gafarta masa zunubansa wadanda suka gabata.


MANZON ALLAH Salallahu Alaihi Wasallam   ya koya wa Nana Ai’sha (Allah ya qara mata yarda) wata addu’a da za ta riqa karantawa a wannan dare.


ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻚ ﻋﻔﻮ ﺗﺤﺐ ﺍﻟﻌﻔﻮ ﻓﺎﻋﻒ ﻋﻨﻲ


“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afuwa fa’afu anni”.


YA ALLAH kasa muna cikin wayanda zasu ga wannan daren dan kaunar Rahamarka da kake yiwa  Annabi Salallahu Alaihi Wasallam.


Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA