GA WASU HADISAN ANNABI S A W MASU MATUKAR MUHIMMANCI

*Mai yakai Hadisan Annibi Dadi?* 



*HADISI NA FARKO
Manzon Allah (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x Allah ya yi masa Alkawarin zai gina masa katafaren gida a gidan Aljanna. Sai Sayyidina Umar ya ce Ai to in haka ne sai mu dinga yawaitawa, sai Manzon Allah ya ce Allah shine mai yawaitawa Allah shine mai tsabtacewa. 

*HADISI NA BIYU
Manzon Allah ya na cewa duk wanda ya karanta suratul Kahfi a ranar jumaa Allah zai cika masa hasken sa har zuwa wata jumaa mai zuwa yana cikin haske yana cikin farin ciki.

*HADISI NA UKU
Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce duk wanda ya haddace ayoyin goma na farkon kahfi Allah zai kiyaye shi daga fitinar Dujjal. 

*HADISI NA HUDU
Manzon Allah yana cewa Wanda ya karanta ayatul kursiyu bayan kowace Sallah ta farillah ba abinda zai hana shi shiga Aljanna sai in bai mutu ba. 

*HADISI NA BIYAR
Idan kazo zaka kwanta a shimfidar ka da daddare to ka karanta kulya ayyu hal kafirun to bazaka mutu mushriki ba  idan ka mutu a wannan daren. 

*HADISI NA SHIDA
Wanda ya yi alwala, bayan ya kare alwala sai ya ce Ash-hadu alla ilAha illallAh wahadahu lasharika lahu wa anna muhammadan Abduhu wara suluhu. Allahumma Ja'alni minattauwabina waja'alni minal mutadhahhirina. 
Duk wanda ya fadi wannan bayan gama Alwalar sa to za'a bude masa kofofin Aljanna guda takwas ya zabi wadda ya ke son shiga. 

*HADISI NA BAKWAI
Wanda ya yi alwala bayan ya kammala alwalar sa kaf, sai ya ce Subhanakallahumma Wabihamdika ash  -hadu allah Ilaha illallah anta astagfiruka wa'atubu ilaika. 
Zaa rubuta wannan acikin wata takarda baza'a bude ta ba sai ranar lahira ya ga alkhairin da ke cikin ta. 

*HADISI NA TAKWAS
Wani Sahabi ya ke cewa wata rana muna tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wasallama sai wani mutum daga cikin sahabbai ya ce Allahu Akbar kabirah, Walhamdulillahi kasirah, Wasubhanallahi bukratan waasilah, Sai Manzon Allah ya ce wanene cikin ku ke fadar wannan kalma, sai ya ce ni ne Ya rasulullah sai Manzon Allah ya ce nayi mamakin wadan nan kalmomi da ka fada, anbude kofofin sama gaba daya saboda wannan kalma da ka fada.  Sai Abdullahi Dan Umar ya ce tun daga wannan rana kullum sai na fadi wannan kalma, ban taba tsallake wata rana ko wani lokaci da bana fadar wannan kalma ba. 

*HADISI NA TARA*
Wata rana mun kasance muna Sallah a bayan Manzon Allah (S.A.W) da Annabi ya dakko daga ruku'u sai ya ce Sami'Allahu Liman Hamidahu sai wani mutum daga cikin sahabbai yace Rabbana Walakal Hamdu, Handan Kasiran Dayyiban Mubarakan Fihi da aka gama sai Manzon Allah ya waiwayo sai ya ce Wanene ya fadi wannan sai mutumin yace Ni ne ya Manzon Allah sai Manzon Allah ya ce Naga Malaika talatin da "yan kai suna rigagato wazai rubuta wannan aiki yaje ya gayawa Allah. 

*HADISI NA GOMA
Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Wanda ya yi sallar nafila rakaa goma sha! biyu tsakanin dare da rana Allah zai gina masa gida a cikin gidan Aljanna. 

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA