DAREN LAILATUL-QADAR

Daren LAILATUL QADR ya fi watanni dubu wanda ba wannan daren a cikinsa alheri, haka Qur’ani ya bayyana alherinsa ya fi na shekara tamanin da wata hudu. Hadisai sun zo suna bayanin samun wannan dare a cikin watan Ramadana ne. Sunna ta tabbatar kamar yadda Allah ya ce; • Kuma ana samunsa a cikin goman karshen Ramadan. • Ana samun wannan dare ne a cikin kwanukan mara, kamar daren 21,23,25,27,29, • Amma an fi sa ran samunsa a daren ashirin da bakwai (wato bayan an kai azumi na ashirin da shida). Amma hadisi ya zo MANZON ALLAH ( Salallahu Alaihi Wasallam ) yace “ku neme shi (daren lailatul qadr) a dare na mara”. An so mutum ya dage da ibada a cikin wannan daren ya raya sa da nau’o’in ibada, kamar karatun Alkur’ani da nafila da zikiri, hakanan ma an so mutum ya umurci iyalinsa da yin ibada a daren su dukkansu. • MANZON ALLAH (S alallahu Alaihi Wasallam) ya ce wanda ya yi tsayuwar daren lailatul qadri Allah ya gafarta masa zunubansa wadanda suka gabata. ...