BISMILLAHIR RAHAMANUR RAHIM WASSALALLAHU ALANNABIYUL KHARIM NASIHA GA MATA A KAN JININ HAILA. HAILA:- (Jinin Al’ada na mata) Jinni ne wanda da kansa yake fitowa daga FARJIN mace wadda a al’ada Zata Iya Daukar Ciki. SHEKARUN DA MATA SUKE YIN AL’ADA Daga shekara tara (9) zuwa goma sha uku (13) in dai jini ya fitowa mace to na al’ada ne ma’ana ta fara al’ada kenan, wato zata iya daukar ciki kenan. LOKACIN DA YAKAMATA A LURA DA SU WAJEN ZUWA DA DAUKEAWAR JININ HAILA. Sune: Daukewar (HAILA (Jinin Al’ada) 1. KAFIN FADUWAR RANA Idan jinin al’ada ya dauke lokacin da mace zata iya yin sallah raka’a “5” kafin rana ta fadi (wato zata sami yin “AZAHAR” raka’a hudu kuma ta yi raka’a “1” daya sallar “LA’ASAR” sannan rana ta fadi). A wannan lokacin dole ne tayi sallar AZAHAR da LA’ASAR na wannan rana. Idan jinin Al’ada ya dauke lokacin da mace zata iya yin sallah raka’a hudu (4) kafin ALFIJIR ya keto dole ne tayi sallar MAGARIBA data ISHA’I ...
FARILLAN SALLAH Shinfida: Ita sallah ibadace mai matukar mhimmanci da kuma girma a wurin Ubangiji mai girma da daukaka, saboda haka ya zama wajibi akan kowanne mutum daga cikin mu ya kyautata wannan sallah ta hanyar cika farillanta da kuma sunnoninta da mustahabbanta. Farillan Sallah: Idan akace wannan abun farillane to dole ka aikata shi, rashin aikatashi zai janyo matsala a wannan ibadar. Idan ake farillan sallah to anan nufin abubuwa masu matsayi na farko a cikin sallah ta yadda rashin aikata wannan farilla yana zama sanadiyyar rugujewar sallar mutum, kenan ya zama wajibi mu san wadannan farillai da kuma yadda ake aikata su a cikin sallah, domin su ko kabali da ba'adi ba'a yi musu, wadannan farillai sune kamar haka: 1. Niyya: Ana kudurta tane a zuciya ba wai ana furtata da baki bane, abinda ake so adaidai lokacin da zaka yi kabbarar harama zuciyarka ta nufaci sallar da zaka yi. Abinda zai nuna maka ba'a furta lafazin Niyyah kuma furtata bashi da tasiri shine; Idan zaka y...
SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH. 1. Abubakar Sadeeq (RA) 2. Umar Ibn Khattab (RA) 3. Usman Ibn Affan (RA) 4. Aliyu Ibn Abi Talib (RA) 5. Talha (RA) 6. Az-Zubair (RA) 7. Abdurrahman Ibn Awf (RA) 8. Sa’d (RA) 9. Sa’eed (RA) 10. Abu Ubaida (RA). Ya ALLAH don isar Annabi (S.A.W) ALLAH kasadamu da rabonka nashiga aljannah.
Comments
Post a Comment