BA SANI BA SABO, KALLI JERIN MANYAN MUTANEN DA AKA GARKAME A GWAMNATIN BUHARI
Yaki da rashawan shugaba Muhammadu Buhari na haifan da mai ido
Tun lokacin da ya dau ragamar mulki a 2015, an damke wasu manyan yan siyasa kan badakala
Anyi lokaci a wannan kasan inda akwai wadanda ba’a iya tabasu saboda manyan miyagu ne, sun fi karfin kowa. Amma wannan gwamnati ta nuna musu cewa lallai ba sani ba sabo, duk wanda yayi ba daidai ba, zai ga ba daidai ba. Ga wani jerin manyan yan siyasan da wannan gwamnati ta garkame :
1. Tsohon gwamnan jihar Adamawa, James Bala Ngilari
A watan Maris, anyi binciken tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala Ngilari, kuma an garkameshi a kurkuku.

2. Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido
Sau biyu jami’an tsaro da kotu na garkame Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido akan rashawa da maganganun tayar da kura a kasa. An gurfanar da a 2015 tare da yaronsa guda 2 akan badakalar N1.35 billion.

3. Gabriel Suswam
Anyi ram da tsohon gwamnan hihar Benuwe, Gabriel Suswam, wanda aka sake yau bayan kwanaki 70 a garkame.

4. Babangida Aliyu
sohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, shi ma ya shiga hannu tare da dan takaran gwamnan jihar, Umaru Nasko, inda aka garkameshi a kotu kafin ya samu beli.

5. Mal. Sambo Dasuki
Tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki har yanzu yana garkame akan badakalar kudin makaman yakin Boko Haram.

6. Alex Badeh

7.Ibrahim El-Zakzaky

8. Nnamdi Kanu
Mai Fafutukar Neman yankin biafara gwabnati ta sakeshi kwanan nan bisa wasu manya sharuda

9. Musiliu Obanikoro

10. Bala Mohammed

11. Fani Kayode

12. Nenadi Usman

13. Reuben Abati

Shin mai zaku iya cewa game da wannan kame da gwabnati takeyi. matabbata Naij.
babu shakka anayi munajin dadi
ReplyDelete