WATA WASIYA DA MANZON ALLAH (SAW) YAYWA ALIYU BIN ABI TALLIB AKAN SADUWA DA MATARKA TA SUNNA



في حكمة مجامعة النساء وهي وصية النبي صلى الله عليه وسلم لعلي بن أبي طالب رضي الله عنه قال النبي :



Acikin hikmar Saduwa Da Maata, Kuma wannan wasiyya Ce Da Daga Manzon Allah swt Zuwaga Sayyidna Aliyu bn Abi Dalib rta.


يا علي لا تجامع المرأة في نظر النجوم فإذا كان فيه الولد يكون كاذبا.


Ya Aliyu kada ka sadu da iyalinka acikin KALLON taurari (wato a sararin samaniya) Idan Aka Samu ciki a wannan Saduwa to zai kasance maqaryaci.


ولا تجامع المرأة في حيضها فإذا كان فيه الولد يكون أبرص وأجذم.


Kada ka sadu da MACE a lokacin haila, idan Allah swt Ya Hukunta samun 'Da to zai kasance da cutar kuturta.


ولا تجامع المرأة والناس يسمعون صوتها فإذا كان فيه الولد يكون سفيها.


Kada ka sadu da MACE alhalin mutane suna Jin sautin ta, idan Allah swt Ya Hukunta samun 'Da to zai kasance Wawa ko gaula ko ga'bo.

ولا تجامع المرأة وقت الضحي والنهار فإذا كان فيه الولد يكون مجنونا.


Kada ka sadu da MACE a lokacin hantsi ko kuma da Rana tsaka, idan Allah swt Ya hukunta samun 'Da to zai kasance Mahaukaci.


ولا تجامع المرأة وهي تنطر النجوم فيكون الولد عاصيا لله ورسوله.



Kada ka sadu da MACE alhalin tana KALLON taurari a sama, idan Allah ya hukunta samun 'Da to zai kasance mai Sabon Allah da Manzon SA.


ولا تجامع المرأة وهي كارهة فيكون الولد عاقا لوالديه.


Kada ka sadu da MACE Akan tilas, idan Allah ya hukunta 'Da to zai kasance mai rashin biyayya Ga mahaifansa uwa da UBA.


ولا تجامع المرأة وأنت تنطر فرجها فيكون الولد أعمي.


Kada ka sadu da MACE kana mai KALLON farjinta, idan Allah ya hukunta 'Da to zai kasance Makaho.


ولا تجامع المرأة ليلة الأضحي ويومها فيكون الولد سفاك الدماء.


Kada ka sadu da MACE daren Babbar sallah da kuma ranar ta, idan Allah ya Hukunta 'Da to zai zamo Dan Ta' adda mai zubar da jini.

ولا تجامع المرأة آخر الأربعاء من الشهر فيكون الولد عدوَّ الله و النبي والمسلمين
Kada ka sadu da MACE a larabar karshen ko wane wata na Musulunci, idan Allah ya Hukunta  'Da to zai zamo maqiyin Allah da Manzon Allah da kuma Musulmi baki daya.




MUNA ROKON ALLAH DA YABAMU IKON KIYAYE WANNAN AMEEN

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA