BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)
BISMILLAHIR RAHAMANUR RAHIM WASSALALLAHU ALANNABIYUL KHARIM NASIHA GA MATA A KAN JININ HAILA. HAILA:- (Jinin Al’ada na mata) Jinni ne wanda da kansa yake fitowa daga FARJIN mace wadda a al’ada Zata Iya Daukar Ciki. SHEKARUN DA MATA SUKE YIN AL’ADA Daga shekara tara (9) zuwa goma sha uku (13) in dai jini ya fitowa mace to na al’ada ne ma’ana ta fara al’ada kenan, wato zata iya daukar ciki kenan. LOKACIN DA YAKAMATA A LURA DA SU WAJEN ZUWA DA DAUKEAWAR JININ HAILA. Sune: Daukewar (HAILA (Jinin Al’ada) 1. KAFIN FADUWAR RANA Idan jinin al’ada ya dauke lokacin da mace zata iya yin sallah raka’a “5” kafin rana ta fadi (wato zata sami yin “AZAHAR” raka’a hudu kuma ta yi raka’a “1” daya sallar “LA’ASAR” sannan rana ta fadi). A wannan lokacin dole ne tayi sallar AZAHAR da LA’ASAR na wannan rana. Idan jinin Al’ada ya dauke lokacin da mace zata iya yin sallah raka’a hudu (4) kafin ALFIJIR ya keto dole ne tayi sallar MAGARIBA data ISHA’I ...

Comments
Post a Comment