Makarantun Da ‘Ya’Yan Shugaba Buhari Suka Yi Da Shekarun Haihuwarsu


Jaridar Premium Times ta wallafa wani sashe na littafin da wani farfesa a kasar Amurka, John Paden ya rubuta akan shugaban kasa Muhammadu Buhari mai suna ‘Muhammadu Buhari: The Challenges of Leadership in Nigeria’ inda suka zayyano makarantun da ‘yayan shugaban kasar suka yi daya bayan daya da shekarun da aka haife su.
GA FASSARAR WALLAFAR:
1. FatimaAn haifi Fatima ranar 7 ga watan Maris, 1975. Ta yi makarantar firamari dinta a firamarin Sojojin Sama da ke Victoria Islands a jahar Lagos, ta yi karatun sakandaren ta a Kwalejin gwamnati dake Kaduna wato Government College, Kaduna; sannan ta yi digirin ta na farko a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria kafin ta tafi kasar Ingila domin yin karatun babban digiri dinta a harkar kasuwanci.
Image result for fatima buhari


2. Nana-HadizaAn haifi Nana Hadiza a ranar 23 ga watan Yuni 1981. Ta fara karatunta ne a Makarantar Essence International School da ke Kaduna sannan ta tafi Kasar Ingila domin Cigaba da karatunta.
Ta yi Karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Buckingham duk a kasar Ingila sannan ta dawo Kaduna domin yin babban digirinta a fannin Malanta a ‘National Teachers Institute’ da ke Kaduna. Ta yi digirin mastas dinta a Kwalejin Kimiyya da fasaha da ke Kaduna (Kaduna Polytechnic).
Image result for Nana-Hadiza Buhari 

3. SafinatuAn haifi Safinatu ranar 13 ga watan Oktoba 1983. Ta yi karatu a makarantar Essence International School sannan ta wuce kasar Ingila domin yin karatu a Cobham Hall, Kent, Jami’ar Plymouth, duk a kasar ingila sannan har yanzu tana karatu a Jami’ar Arden da ke kasar can.

4) HalimaAn haifi Halima ranar 8 ga watan Oktoba 1990. Tayi Makarantar Essence International School, sannan ta ci gaba a makarantar British School of Lome; Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Leicester duk a kasar Ingila. Daga nan ta dawo makarantar koyan aikin lauya a Nijeriya.
Image result for Halima buhari

5) Yusuf: An haifi Yusuf a ranar 23 ga watan Afrilu. Ya yi karatunsa ne a Kaduna International School; British School of Lome; Kwalejin Bellerby’s da Jami’ar Surrey, duk a kasar Ingila.
Image result for Yusuf buhari

6) ZahraAn haifi Zahra ne ranar 18 ga watan Disemba 1994. Ta yi karatunta a makarantar Kaduna International School; British School of Lome; Kwalejin Bellerby’s da jami’ar Surrey duk da ke kasar Ingila.
Image result for Zahra buhari
Image result for Zahra buhari
Image result for Zahra buhari

7) A’isha (Hanan): An haifi A’isha ranar 30 ga watan Agusta 1998. Ta na karatunta a makarantar Kaduna International School.
hanan-buhari1

8) Noor (Amina)An haifi Noor ranar 14 ga watan Satumba 2004. Ta na karatun ta a Kaduna International School.
Babbar ‘yar Buhari mai suna Zulaihat ta rasu a shekara ta 2012 a dalilin ciwon ‘sickle cell anemia’ a yayin nakuda. Kafin nan iyalin Buhari sun rasa yaro namiji mai suna Musa, a lokacin da ya na jariri shi ma a sakamakon ciwon na’sickle cell anemia’

Comments

Popular posts from this blog

FARILLAN SALLAH

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH