WASU DAGA CIKIN MU’UJIZOJIN ALKUR’ANI (1)
WASU DAGA CIKIN MU ’ UJIZOJIN ALKUR ’ ANI (1) Manzannin da Allah (SWT) Ya aiko tun daga Annabi Nuhu (AS) zuwa kan Annabinmu Muhammad (SAW) kowa da irin baiwar da Allah kan zaba Ya kebance shi da ita, don ya zamo darasi da kuma nuni ga mutanensa cewa daga Allah yake. Amma kowane Manzo mu ’ ujizarsa tana shudewa ya zamo sai labarinta, amma ban da Alkur ’ ani. Ga misalai kamar haka: Annabi Sulaiman (AS) yana da mu ’ ujizozi masu yawa, daga ciki ya yi magana da tsuntsaye har da tururuwa kamar yadda ya zo cikin Alkur ’ ani a Suratun Namli aya ta 17: “ Kuma aka tattaro wa Sulaiman rundunoninsa daga aljanu da mutane da tsuntsaye, kuma aka kange su cikin ayari. Har lokacin da suka iso kan rafin tururuwa, sai wata tururuwa ta ce, “ Ya ku jama ’ ar tururuwa! Ku shiga gidajenku kada Sulaiman da rundunoninsa su tattake ku, alhali ba su sani ba. Sai ya yi murmushi yana mai dariya daga maganarta, kuma ya ce ya Ubangijina Ka cusa mini godiya ga ni ’ imarKa wadda ka ni ’ imta g...