YADDA MARIGAYI ABUBAKAR AUDU YA RASU:
YADDA MARIGAYI ABUBAKAR AUDU YA RASU:
Marigayi Prince Abubakar Audu, dan takarar gwamnan jihar Kogi karkashin tutar jamiyyar APC a zaben da aka gudanar jiya Asabat. Allah ya karbi rayuwarsa ne a wannan rana.
Bayanai daga Iyalan marigayin na nuna cewa:
Marigayin ya fara Aman Jini ne a ranar Juma‘a da Daddare.
Wadda suka bayyana hakan da Alaka da hawan jini.
“Marigayi Abubakar Audu ya tashi wayewar garin jiya Asabat ne cikin rashin jin dadi.
Amma Likitansa ya bashi wasu maganunuwa, wadda hakan har ta sanya masa zuwa wajen kada kuri‘arsa na zaben gwamnan jihar a mahaifarsa dake Ogbonicha.
Bayan dawowarsa gida a jiya Asabat din, ya cigaba da yin Aman, inda lamarin yayi kamari gabannin wayewar garin wannan rana ta Lahadi.
Bayanai dai sunce Marigayi Prince Abubakar Audu, ya rasune tunda misalin karfe 5am na safiyar wannan rana, kafin hukumar zabe ta fara tattara sakamakon zaben da aka gudanar jiya Asabat.
Marigayi Abubakar Audu ya mulki jihar Kogi tsakanin Shekarar 1999 zuwa 2003.
Hukumar Zabe ta INEC dai a yau ta sanarda cewa: Zaben da aka gudanar jiya Asabat, bai kammala ba. Amma dai Marigayi Abubakar Audu ne ke kan gaba.
Allah yajikan Abubakar Audu, yasa Aljanna ta zame masa makoma! Muda muke hanya idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani.
allah yajikan sa
ReplyDeletealh ya jikan shi
ReplyDeleteALLAH YA MASA RAHAMAH
ReplyDelete