LOKACIN SANYI
HUKUNCE HUKUNCEN LOKACIN SANYI !!!
Magabata na Kwarai sun kasance suna Murna da shigowar lokacin sanyi, Saboda Dare yana tsawaita, Yini kuma yana gajarcewa, Hakan yana basu isheshen lokacin Sallar Dare da kuma Azumtar Yini.
Manzon Allah(SAW) yace:
“Azumi cikin Sanyi, Ganima ce Sassanya” Ahmad Albani ya inganta.
Abdullahi Bn Mas’ud yana cewa : “Maraba da shigowar Hunturu, Albarka za ta sauka, Dare zai tsawaita, Yini zai gajarce don Azumi” Cikin Abubuwan da ake so ko ya halatta lokacin sanyi:
1. Gaggauta yin Sallah. Manzon Allah (SAW) idan Lokacin Sanyi ya shigo yana Gaggauta Sallah. Adabul Mufrad.
2. Kashe wuta Musamman in za a kwanta don lokaci ne na Gobara.
Manzon Allah yace:
” Wannan Wutar Abokiyar gabarku ce, in zaku kwanta ku Kashe ta”
3. In sanyi ya tsananta za a iya hada Salloli, Hakama Jam’i zai iya faduwa akan Masallaci.
“Manzon Allah (SAW)ya kasance yana sawa a yi kiran Sallah a cikin daren da ake tsananin Sanyi da kowa yayi Sallah agidansa” Ibn Maja.
4. Halaccin shafa a kan Huffi, Safa, Rawani, da Khimarin Mata matukar cireshi zai wahalar.
5. Lokaci ne na kadawar Iska, In har ta taso, kar a manta da Addu’ar da Manzon Allah ya karantar: “Allahumma Inni As’aluka khairha wa khaira ma arsalta bihi, Wa a’uzu bika min sharriha wa sharri ma ursilta bihi”
Allah ya sa mu dace da Sunnar Annabi (SAW)
ameen
ReplyDelete