HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI A KODA YAUSHE

HANYOYI 15 DA ZAKA SA MATAR KA CIKIN FARIN CIKI A KODA YAUSHE:

1- Idan ka shiga gidan kace Assalamualaikum' shaaidan zai bar gidan! 2- Ka rika yawan bata labarai.

Saboda Allah (S.w.t) ya sanar da mu dan Adam yana son labari.

3- Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta ka nuna 6acin ranka.

4- Ka zama mai yawan bata kyaututtuka. Kyauta tana kara dankon soyayya.

5- Ka share wasu daga cikin kuskurenta. Ka nuna baka ma san ta yi ba. Kuma ka dauka a matsayin abinda ya shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka.

6- Ka nuna mata tausayawarka gareta a fili, musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al'ada. 7- Kada ka daukaka abokanka fiye da matarka.

(lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana,a sama da matansu)

8- Ka nuna mata babu wata budurwa dake gabanka sai ita, Ka nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurinka.

9- Ka rika tunawa da ita a cikin addu'arka. Hakan zai kara kauna tsakaninku.

10- Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kyatayi da kake mata, kamar siyan abinci,Saboda daman hakkinta ne ka kawo mata,sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.

11- Shaidan ne abokin gabarka ba matarka ba,Lokuta da dama idan mata da miji suka dan samu sa6ani har takai ana maida martani cikin fushi,To katuna ba daga ita bane shaaidan ne ke zugata, Saboda shi yana mutukar son ayi saki.

12- Ka dauki abinci ka saka mata abaki. Annabi (s.a.w) ya ce, "abincin ba cikinta kadai zai shiga ba, zai huce har zuwa zuciyarta."

13- Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/ fara'a domin Manzo (s.a.w) ya ce: "Duk wanda ya nunawa matarsa fara'arsa to dai-dai yake da yin sadaka."

14- Ka zama mai yawan neman shawararta. (wasu suna ce wa ba,a shawara da mata). To ku sani ce wa manzo (s.a.w) ya kasance yana shawara da matansa.

15- Kar ka Boye mata damuwar ka, farin cikinka ko bakin cikinka. Domin ita magani ce a tattare dakai.

ALLAH yasa mu dace da mata nagari ameeeeen

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA