YAR UWATA KINSAN WANNNAN KUWA

*Kyau shi yake rudin maza, amma Ilimi shi yake sawa ajima ana tare?

*Yanga shi yake rudin maza, amma iya magana ne yake gamsar dasu? *Jan aji yana qara miki aji a gaban mutane, yawan surutu yana sanyawa a raina ki?

*Gaskiyarki tana qara miki qima a gaban mijinki, Karya tana yarfa ki da rage miki kima?

*Zuwa da budurcinki gidan mijinki shine kawai 'yancinki, da zarar kin wulaqanta shi kin shiga matsala, kin gamu da wulaqanci da gori na har abada?

*Bayyana sirrin aurenki babu inda zai kaiki, 6oyeshi tare da magance shi tsakaninki da maigida shine kawai mafita a gareki?

*Idan kika bawa kudi zuciyarki, zaki wulaqanta, idan kika baiwa Allah zuciyarki zaki samu kulawa na har abada?

*Tara mazaje babu inda zai kai ki, za6en daya tamkar da goma shine mafita?

*Yawan dariya ko murmushinki zai sanya maza su raina ki, kama kai da maintaining zai qara miki girma?

*Haquri da na gidanku shine mutuncinki, sa ido kan abin hannun maza babu inda zai kaiki?

...Ko wacce mace sarauniya ce sai dai wacce tayi wasa da damarta,ta wajen furta kalaman da basu chanchanta ba, ko kuma yin abin da bai kamata ba... 'YAN UWANA MATA ALLAH YASA KUN FAHIMCENI. AMIN

Comments

  1. Maryam muhd s.lawan25 April 2016 at 00:28

    Gaskia mungode amma meyasa inbaka kula wasu mazan da mata kake riqe mutuncinka akema kallon kaci ka girman kai da yanga,don nima anmin tambarin duk wanda|wacce zatai tare dani sai tabini kamar rakumi da akala kuma saita zubar da hawaye dan kawai ba kowa nake kulawaba,kuma abin nadamuna

    ReplyDelete
  2. wannan gskyne ammanfa idan kanayin wannan abu dayawa mutane kece waka cika girman kay maiyasanyah haka?

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA