SOYYAYA A PRISON
SOYAYYA A PRISON
Labarin Wata budurwa da akayiwa sharri kisan kai, akaje kotu Alkali ya yanke mata hukuncin daurin rai da rai prison. Aka kai ta prison bayan ta shiga bata da wani aiki sai kuka, ana nan sai wani mutum da yake aiki a prison din, aikinsa kawai idan mutum ya rasu yazo yayi dawainiyar sanya mamacin a akwatu a rufeshi.
Sunnan aje a bunne gawar. Kullum sai ya ganta tana kuka har watarana yaje ya tambayeta ta kwashe Labarin ta kaf tagaya masa, tace kuma kukan da takeyi kako yaushe idan ya shigo sai yazo wajenta sun gaisa yana dai dan debe mata kewa, har soyayya ta shiga tsakanin su sosai har suna cewa ba wanda ya isa ya rabasu Tab. Sai dai kuma tayaya xasuyi auren? Wata rana suna hira sai tace yakamata mu san yanda zamuyi na kubuta muje muyi Aure sai yace mata to yaza ayi, sai ta bada shawara cewa
IDAN ANYI MUTUWA A GIDAN ZATA JE TA SHIGA CIKIN AKWATIN DA GAWAR TAKE IDAN YAZO SHI DA YARANSA SAI YA RUFE KAWAI IDAN AKA BINNE SU SAI YAJE DAGA BAYA YA TONE TASU GUDU,
ya amsa yace toh haka za ayi, kawai idan anyi rasuwa kije ki shiga.
Bayan kwana Biyu da magariba akayi rasuwa a prison din kawai ta tashi ta gano inda gawar take ba tare da ta nemi inda yake ba tunda dama da alkawarin kawai ta dau wata yar karamar touch light ta tafi dakin da gawar take ba tare da duba Gawar mace ko namiji ba, kawai ta kwanta kusa da ita acikin akwatin TOFA Yaransa na xuwa sai suka Bin ne gawar suka dawowar su prison wohoho. . . Ta dan jira kadan bataji yazo ya toneta ba sai ta fara yiwa axuciyar ta Tambaya cewa:- Ace dai yaki zuwa ya tone ni tab! !) sai tace bari dai na duba gawar nan namiji ne ko mace sai ta xaro touch light din nan tayi yan dabaru ta haska fuskar gawar kwatsam sai taga ASHE SAURAYIN NATA NE YA RASU. . . . . . .
jama'a ina mafita
hahahahaha shikenan aikin Gama ya gamu
ReplyDeleteshine kenan abun nema ya samu. sai su ci gaba da soyayyar su a kabarin. ma'asalam.
ReplyDelete