NIMA AURE NAKESO.
KEMA AURAN KIKE SO
Nakan sha mamaki a duk lokacin da na ji mata suna tattauna maganar da ta shafi Aure, musamman idan na ji sun zake wajen nuna bukatuwarsu ga Auren.
Jiya ma haka na ji yan Mata uku suna tafiya suna maganar Auren wata kawarsu da ya gabato, ba wai maganar irin hidimar da suka tanadarwa bikin ba ce abinda ya ja hankali na, a'a, kokawar da dayarsu take yi dangane da rashin samun tsayayyen saurayin da yake sonta da gaske kuma zai aure ta.
"Ki duba yadda nake da kyau, kuma ina da kokarina daidai gwargwado, amma wai har WANCE........ ta samu Mijin Aure ni kuwa shiru, wallahi da akwai yadda zan yi a fasa Auren in ya so kowa ya rasa da zan yi".
Sai dayar ta ce:
"Da ni fa ya nuna yana so amma ban ba shi fuska ba saboda na ga ba kala ba ne, ga shi na tsaya kallon ruwa kwado ya min kafa. Kuma kin san abinda ya fara hada mu da shi, wai ni zai yiwa wa'azi na daina kula samarin ajinmu".
Sai ta ukun ta ce:
"Ku dai kawai ku yi fatan Allah ya ba su zaman lafiya muma Allah ya ba mu nagari, kuma wallahi inda zan samu irin wannan saurayin shi nake so".
Sauran kadan na yi karambanin yi wa ta ukun magana, amma sai zuciyata ta gargade ni.
Wannan sai ya tuna min da wata fira da na ji mata suna yi a daya daga cikin jami'o'in Arewacin Kasar nan; a shekarar 2008 inda na riski wasu mata suna fira, daya daga cikinsu ta ce:
"Ni kam wallahi idan na samu miji barin bokon nan zan yi na yi aure na, ku duba yadda na kode, fata ta har ta gaji da shafe-shafe amma ba labari".
Idan na fahimci bayanan Matan nan daidai, kamar suna so su nuna Maza suna d'an wuyar samu, kuma koda kina da saurayi matukar ba aure kuka yi ba, to zai iya sauya sheka zuwa ga kawarki.
Idan lissafina ya yi daidai, to me yake kawo hakan? Kadan daga cikin dalilan ba za su rasa nasaba da irin wulakanci ko raina ajin Saurayi idan ya tallata soyayyarsa ga Budurwa ba, wasu kuma kan kin nunawa saurayin soyayya har sai ya gaji ya koma kan wata.
To ina ganin idan haka ne, yana da kyau mata su rike samarinsu da soyayyar gaskiya, su sanya tsoron Allah kan lamuran neman aure, kada su raina dukkan wanda ya nuna musu soyayya.
Dangogin ma'auratan su sassauta, hakika al'adun da suka kanannade aure su suka kawo masa tarnaki. Akwati daya da yan turame biyar ma sun isa, Albarka ake nema a Aure.
Maza da matan kowa na matukar son aure fiye da tunanin iyaye.
To ALLAH ne yasan karatun Kurma Ya ALLAH kasa kuma matan Ku gyra kuskuranku
Amin summa amin.
ReplyDeleteInason wanda takesona ga number na sai ki kirani(08101989902)
ReplyDeleteHM
ReplyDelete