KISAN SIR. ABUBAKAR TAFAWA BALEWA
KISAN SIR ABUBAKAR TAFAWA BALEWA. Na John McIntosh ( Baturen Ingila masanin tarihin Nijeriya)
Bayan sun kamoshi (Sir Tafawa Balewa) suka (daureshi a cikin mota suka yi ta jansa a kasa suna cikin mota inji Dan Masanin Kano) suka zagaye wasu wurare cikin Lagos dashi kafin su zarce bayan gari dashi.
A can ne suka azabtar dashi, suka nakada masa bugun tsiya suka wulakantashi. Sannan suka tilasta masakurbar barasa da zukar sigari - Abubuwan da bai tabayi a rayuwarsa ba kasantuwarsa musulmi mai riko da addinin.
Bayan sun kammala muzgunamasa, sai ya rokesu alfarma da su barshi yayi sallah ta karshe kan su kasheshi tunda ya tabbatar kasheshi zasu yi. Nan take a wulakance suka bashi izini.
Bayan ya idar da sallar sai ya dubesu yace " Iyamuri ! Iyamuri ! Iyamuri !" Ya cigaba da cewa da yardar Allah ba zasu taba mulkar Nijeriya ba, zasu tarwatsu, za a tsanesu duk inda suke, zasu yi fama da bakin ciki iri iri da bala'oi, zasu yi fama da gaba daga sauran yan kasa. Bayan ya gama sai ya kallesu a jarunce yace " Yanzu zaku iya kashe Firayin Ministanku" A cikin wannan yanayine Sir Abubakar Tafawa Balewa ya rasa rayuwarsa a hannun matasan hafsoshin sojan Iyamurai karkashin Manjo Emmanuel Ifeajuna da Kyaftin Okafor a Legas daren 15 Janairu 1966.
*Allah Ka Jikan Sir. Abubkar Tafawa Balewa....
Allah ya gafarta masa
ReplyDelete