YADDA AKE HADA BONVITA CIKIN SAUKI
YADDA AKE HADA BONVITA KAYAN DA AKE BUKATA: Sukari Ruwa Cocoa Madara ta garai Fulebo na gari YADDA AKEYI. Asamu roba mai fadi a auni sukari gwan-gwani daya {1} sai a auni ruwa chokali biyu {2} sai a hada a cakuda sosai sai a auni cocoa chokali biyu {2} sai madara ta gari chokali daya {1} ko chokali biyu{2} sai a auni fulebo yadda ake bukata. Sai a chakudasu waje daya sosai sai sun hada jikinsu sosai asami faranti ko leda mai tsafta a baza asa arana. Duk bayan minti goma {10} sai a juya shi har saiya bushe sosai. Shikenan bonvita ya hadu.
Comments
Post a Comment