RUNDUNa ta goma

******RUNDUNA TA GOMA********** KA KARANTA A NUTSE. A lokacin da aka kasha ka’abu sai yahudawa suka dora wani kafiri mai suna asiru a matsayin ka’abu. Bayan an nada wannan shuga ba ne sai manzon allah {saw} ya umarci wasu daga cikin musulmai cewa suje su nemo labarin wannan sabon shugaba koda suka je sai suka samu labara cewa wannan shugaba yayi alkawari cewa zai yiwa manzo allah {saw} abin da ba’atabayiwa halitta irin wannan cutarwa ba. Ya ce don haka yanzu zanje garin gadafana in tattaro mutannan nahiyar baki daya su zo domin mu yaki manzon allah {saw}. Nan take sai wannan kafiri ya nufi wancan gari da ya ambata don gaiyato wadancan matsiyata “yan uwansa, sukuma sahabbai da suka ga haka sai suka juya suka sanar da manzon allah {saw} abin da sabon shugaban kafirai ya shirya. Batare da bata lokaci ba sai sai manzo allah {saw} ya shirya sadaukai tallatin abisa karkashin jagorancin abdullahi dan rawaha, suka fito don su hana wancan fajiri zuwa garin da ya nufa. Koda suka hadu da wannan kafiri a daidai haibara. Sai suka nemieshi cewa idan zai yarda to yazo su koma wurin manzon allah {saw} kada yaje wurin wadan can kafirai, idan ya aminta za a bashi sarkin haibara nan take wannan kafiri ya amsa shima dai a lokacin yana tare da yahudawa yan uwan su talatin wato adadin yawan yanda mulmai suka fito a lokacin. To lokacin da ya mika wuya sai kowane musulmi ya riki kafiri daya suka ci gaba da tafiya. Suna cikin tafiya ne sai wannan kafiri ya canja shawara a cikin zuciyarsa, don haka sai shi yayi niyyar kubbucewa daga hanun abdullahi harma yayi yunkurin kwace tokobinsa . Amma ina allah bai bashi saa ba sai abdullahi yace da shin i zaka yaudara ya kai makiyin allah? Sai abdullahi ya sako daga kana bin hawansa ya kaiwa wannan kafiri sara, nan take ya kasha shi, suma mulmai suka din ga kasha na hannayensu sai da suka kashesu baki daya. ==========WANNAN SHINE SAKAMAKON MAYAUDARI========= TO mai kartu a nan zan dakata sai wani karon zamu kawo muku yake-yake sayyidina abubakar da yadda shima yasha gwagwar maya.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA