HADISINMU NA YAU.

Abu Huraira (RA) yace: Watarana na tambayi Manzon Allah s.a.w cewa, “Ya Rasulillah, wanene acikin mutane zai fi kowa kasance wa acikin farinciki wanda zai fara samu samun ceton ka a ranar lahira?” sai Manzon Allah s.a.w yace, “Ya kai Abu Huraira, a tunani na babu wani mutum da zai Sake yi mini irin wannan tambayin bayan kai, saboda a yadda nake gani kai kadai ne mutum na farko da ya fara bayyana niyyar sa a fili zuwa ga hardace maganganu na. Mutum na farko mafi farinciki acikin mutane da zai fara samun cetona a ranar lahira shi ne mutumin da ya furta kalmar LA'ILAHA ILLALLAH da gaskiya har ya zuwa acikin zuciyar sa.” : Hadisin: Sahih Bukhari na 99. : Allahu Akbar Ya Allah kasa muna daga cikin ire- iren wadannan mutanen. Allah ka sada mu da rahamar ka a duniya da lahira.. @Ya Allah kasa mu dace da samun ceton Manzon ka, kuma Bawan ka Muhamadur Rasulullah )s.a.w( a ranar lahira..

Comments

Popular posts from this blog

FARILLAN SALLAH

BAYANI AKAN JININ HAILA (JININ AL'ADA)

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH