HADISIMU NA YAU
Abdullahi Ibn Mas’ud (RA) yace: Watarana Manzon Allah s.a.w, ya fitar da zakkah yana rarrabawa mutanen garin madina sai wani mutum daga cikin jama'ar Ansar yace, “Wallahi ina rantsuwa da sunan Allah, Muhammad bai yi niyyar fitar da wannan zakkar da yake rabbawa jama'a ba acikin farinciki ba!” Abdullahi Ibn Mas'ud (RA) yace da naji haka sai na zo wajen Manzon Allah s.a.w na labarta masa abin da naji mutumin nan ya fada, nan take sai na ga bacin rai ya bayyana a fuskar sa, sai Manzon Allah s.a.w yace “Annabi Musa ma an cutar dashi da irin wannan hanyar, amma duk da hakan ya daure yayi hakuri.” ¤ ¤ ¤ Hadisin: Sahih Bukhari na 5749. ¤ ¤ ¤ Allahu Akbar Ya Allah ka kara muna hakuri, da Imani acikin zukatan mu. Ya Allah ka kara muna so da kaunar Ma'aiki, tareda yin koyi da kyawawan dabi'un sa. Ya Allah ka karbi tuban mu, kuma ka gafarta muna dukkanin zunuban mu na farko dana karshe # Ameen
Comments
Post a Comment