GARABASA GUDA BIYAR.
GARABASA GUDA BIYAR GA DUK WANI MU'MINi 1- Ko kasan cewa yayin idar da kiran Sallah karka haramtawa kanka Addu'ah , domin Addu'ah a wannan lokaci ba'a juyata..??? * * 2- Ko kasan ina ake sanya zunuban ka yayin da kake sallah..??? Manzon Allah (saw) yace:- "Duk lokacin da bawa ya ke Sallah ana sanya dukkan zunuban sa a wuyan sa da kafadun sa, duk lokacin da yayi ruku'u ko sujada zunuban sa za su dinga fadowa kamar yadda ganye yake fadowa daga bishiya ." Yakai wanda kake gaggawa yayin ruku'u ko sujada, ka tsawaita sujada da ruku'u domin zunuban ka su ragu kada ka bari wannan garabasa ta wuce ka. * * 3- Ko kasan wata salihar mace ta rasu, duk lokacin da 'yan uwanta suka ziyarci kabarin ta sai suji kamshi yana tashi, sai suka tambayi mijinta sai yace ta kasance tana karanta Suratul Mulk kowane dare kafin tayi bacci..??? * * 4- Ko kasan karanta Ayatul Kursiyyu bayan kowace sallah zaka wayi gari tsakanin ka da Aljannah mutuwace kadai..??? * * 5- Ko kasan idan ka idar da sallah kar kayi gaggawar tashi, domin mala'iku suna roka maka gafara..??? Allah ka sanya tunatarwannan tazama SADAKATUL JARIYA a gareni da Iyayena da duk wanda ya taimaka wajan yadawa, Ameeen
Comments
Post a Comment