fish cake
FISH CAKE 〰〰〰〰〰〰〰 Fish( titus) Irish potatoes Egg Butter Milk Dried bread Pepper( fresh) Onion Curry Spices Salt Vegetable oil 〰〰〰〰〰 Da farko, za ki dafa dankalinki a gudan shi bayan kin feresu. Sai ki silala kifinki ki ajiye gefe daya. Sai ki fasa kwai daya a roba daban,ki zuba madara cikin cokali biyu(liquid )sai ki saka bota cokali daya, sai ki kadasu sosai. Sai ki jajjaga albasa da attarugu, sai ki dauko dankalinki ki daddaka yayi laushi, shi ma kifin ki cire kayarsa ki daddaka shi yayi laushi. Sai ki hada kifi da dankali da kayan miya da "batter" wato hadadden ruwan kwai, sai ki saka curry da gishiri da maggi ki cakudasu. Sai ki murmursa busasshen burodi a roba, sai ki dora mai a wuta, sai ki debo hadinnan ki dan yi fadi da shi kamar kwabo, sai ki juya shi cikin garin burodi sai ki jefa shi cikin mai ya soyu. Haka za ki ta yi har ki gama. Ana hada wannan kosan kifi da kunun tsamiya da ya ji kayan kamshi, kuma baa zuba sugar a kunun, foster clark coconut flavour ne sugarki. A ci dadi lafiya. Gobe idan Allah ya kai mu ARABIAN COCKTAIL za mu koya.
Comments
Post a Comment