BUHARI ZAIYI BINCIKE
BUHARI ZAI BINCIKI KUDADEN DA'AKA SACE MILLIYAN 6.9 A GWAMNATIN JONATHAN •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• •••••••••••• Acikin wata bincike the gwamnati ta gudanar ta tono wata sata da akayi da ya kai Dala Miliyan 6 wai domin siyan wajen tsayawa na musamman domin gudanar da jawabi ma shugaban kasa Jonathan. . Bincike ya nuna cewa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a wancan lokacin Mr. Gordon shine ya shiryo wannan cuwacuwa, shi kuma shugaban kasa ya bada izinin fitar da kudin ita kuma Diezani ta bada kudin ta wata asusun kamfanin mai NNPC ta kasa dake wata banki a kasar Amurka. . Ko da yake ba'a siya taburin ba amma dai kude tuni an waske dasu. . A shirin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yake na ganin ya kawar da rashawa da cin hanci a kasar nan, wata sabuwar badakala ta sake bullowa na bincikar gwamnatin Goodluck Jonathan, inda Buhari ya fara shirin bincikar Jonathan da wasu mukarrabansa guda biyu kan kudi dala milyan 6.9 na sayen na'urar jawabi a wurin taro, wato 'mobile stages' a turance, kamar yadda majiya daga fadar gwamnatin tarayya ta bayyana. . An cire kudin ne a asusun ma'aikatar man fetur din Nijeriya, wato NNPC. . Kamar yadda jawabin ya bayyana, lamarin wanda yake da bukatar bincike, za a tuhumi Jonathan, mai kare lafiyarsa, Mista Gordon Obuah da kuma tsohuwar ministar man fetur, Diezani Allison- Madueke. . Majiyar ta kara da cewa an ciri dala milyan 6.9 din ne domin sayen na'urar har guda uku, don yin amfani da su a yayin da Jonathan zai gudanar da taro. . Saidai bincike ya nuna cewa duk cewa an ciri kudin ne da sunan sayen wadannan na'urori, har zuwa yanzu ba saye su ba, wanda hakan ya sa gwamnati mai ci ta waiwayi lamarin, don sanin inda aka karkatar da kudin. . KO KUNA GANIN YA DA CE ATSANANTA BINCIKE A GWAMNATIN JONATHAN?
AH MANA INDA KUDIN BANA GIDANSUBANE
ReplyDelete