ZUWA GA YAN MATA TA MATASA
WASIKA ZUWA GA MATASA MASU aikata istimna'i Assalamu alaikum. ISTIMNA'I = fitar da mani ko sha'awa da gangan ta hanyar da bata dace ba. ya rubuto wannan nasihar ne sakamakon yawan wasikun da muke samu daga Matasa Maza da mata, suna neman taimako akan illolin da suka samu ajikkunansu. sakamakon Istimna'i wato Masturbation. Wannan harkar, Mu anan shafin munyi bayani akanta yafi sau ASHIRIN. Mun kawo hujjoji gamsassu daga Alqur'ani da Sunnar Ma'aikin Allah (saww) da fatawoyin Amintattun Malamai duk akan HARAMCIN ISTIMNA'I. Amma duk da haka wasu matasan basu yarda sun dena ba. Wasu kuwa sunji tsoron ALLAH sun riga sun dena. Babban dalilin da yake janyo musu afkawa cikin wannan bala'in shine : 1. Kallon Fina-finan batsa. 2. Shiga shafukan internet na batsa. 3. Yin zantukan batsa tsakanin saurayi da budurwa. 4. Kusantar zina ta hanyar kallo da shafa, ko zance da dai sauransu. Wasu kuma suna aikata hakan ne don gudun afkawa ZINA, basu san cewa shi dinma ZINAR bane!! Idan kun Qi bari domin Allah, to ku dubi irin illolin da yake haifar muku ajikinku mana!!! 1. MUTUWAR IDANU. 2. MUTUWAR AL'AURA. 3. CIWON BAYA. 4. BUGAWAR QIRJI. 5. RIKICEWAR TUNANI. 6. YAWAN MANTUWA. 7. KARANCIN 'YA'YAN MANIYYI. 8. SAURIN INZALI. 9. SHAFAR ALJANU, ETC. Wadannan 'yan kadan ne daga cikin Matsalolin da ISTIMNA'I yake haifarwa. kuma duk wanda bai tuba ya dena ba, idan ya mutu ahaka zai je ya tarar da hisabi. DON GIRMAN ALLAH!! Matasa ku kiyayi zina da duk dangoginta. ku kaurace ma duk wani abinda zai rika motsa muku sha'awa. Idan da hali kuje kuyi aure. idan kuma babu hali, to ku yawaita azumi. ALLAH YA SAWWAKE.
Comments
Post a Comment