RUNDUNA TA TAKWASA
<<<>>>> RUNDUNA TA TAKWAS <<<>>> KA KARANTA CIKIN NUTSUWA Ita dai wannan runduna manzon allah (saw) ya shiryata ne a ccikin watan sha’aban a karkashin jagorancin abdurrahaman dan auf domin su je su yaki “yan kabilar bani kalbu a cikin garin danmatul jandali, wani babban gari ne. kafin wannan runduna ta tafi sai da manzon allah (saw) yay i musu wasiyya kamar haka: “ku yi yaki gaba dayanku domin daukaka Kalmar allah ku yaki duk wanda ya kafircewa allah kada kuyiwa wani kisan gilla kada kuyi zalunci kada ku kasha yara kanana.” To bayan manzon allah (saw) yayi musu nasiha sai ya mika tuta ga shugaban runduna. Nan take suka mika suka nufi garin makiya allah. A lokacin da suka shiga wannan garin sai da sukayi kwana uku suna kiransu zuwa ga musulunci to a rana ta hudu sai sarkin garin ya musulunta mai suna asbagu dan umar. Kuma an samu mafiya yawa daga cikin muta nan sa sun musulunta. A inda sukum yan ragowar wa yanda basu musulunta ba suka ce sun amince zasu dinga bada dizya. A daya bangaren dai sai shugaban wannan runduna wato abdurrahaman dan aufu ya auri yar wannan sarki kamar yada manzon allah (saw) ya umar ce shi da yin hakan, domin yin hakan wata siyasace da zata kara zumunci a tsakanin sarkin da kuma musulmai kuma yin hakan shi zai hana kawo wata Baraka daga shi sarkin. To haka dai musulmai suka dawo garin madina suna masu cin nasara da farin ciki a cikin wannan tafiya mai dubin albarka. Wannan shine karshen gwagwarmayar RUNDUNA TA TAKWAS in allah yaso zamu kawo muku runduna ta TARA ku kasance damu Ku kasance damu ta wannan shafi mai albarka don samun abubuwa daban daban. Wato @[174223056110540:0]
Comments
Post a Comment