allahu akbar
Imam Shafi'I yana cewa:
"Mun nemi hanyar da zata sa mubar aikata ZUNUBAI.... Sai muka same ta cikin SALLAR WALAHA (salatul-dhuha tana taimakawa bawa wajen barin aikin sabo).
Mun nemi hanyar da zamu sami HASKEN KABARI.... Sai muka gano cikin karatun ALQUR'ANI...
Mun nemi hanyar TSALLAKE SIRADHI (cikin sauki) sai muka gano ta cikin yawan AZUMI da SADAKA.
Mun nemi hanyar da zamu dace da shiga INUWAR ALLAAH.... Sai muka sameta cikin yin ABOTA da mutanan kirki.
Yan' uwa, muyi kokarin aiki da wannan tunatarwar, za muci riba duniya da lahira in shaa Allaah!
barnstormer
ReplyDelete