ZAMANI NE KO KUWA DAI MATAN NE.
ZAMANI NE KO KUWA DAI MATAN NE...............................??????
A shekarun baya da suka wuce,da zarar ansa ranar Bikin
Yarinya,shike nan zakaga ta shiga damuwa,da Jin kunya da
kuma Tsoro.
Wacce bada dadewa ba zata zama Amarya,sai kaga tana
tsananin Jin Kunyar duk wani wanda yake da alaka da Angonta
na gobe,ga kuma kokarin koyan abubuwa wanda zasu
banbanta ta da kananan Mata ko ince kannenta.
Ana cewa watan ko satin Auren yazo,Iyayenta zasuyi Kokari
suganta an kebe ta a Gida babu yawan fita babu Gaira ba
dalili,ko dan tsoron kada wani yaje ya Sace mata zuciya ko ya
yaudareta ko kuma dai wani Mummunan abu ya faru da ita.
A lokacin Bikinta kuwa,zaiyi wahala ba kuka zakaga tana tayi
ba, harma a lokacin ana yin waka ga Amare ana cewa:
"Taqi Ci taqi Sha Sai Dan Karen Kuka".
Wan nan kuma ance saboda abubuwa ne guda biyu yake
sanyata haka:
1=Bakin ciki da kuma Tunanin Rabuwa da Iyayenta da kuma
daukacin danginta,ta koma taje ta hadu da wasu mutanen
nada ban,koda kuwa Auren Zumunci ne za'ayi mata.
2= Tsoron yanda zata sami Mijin,a wajen hali da kuma
bukatarsa ta Aure,ka kuma tsoron rashin tabbas a
rayuwa,wanda zakaga ta RAME sosai a cikin Lokacin yin Auren.
Amma rayuwar mu ta yau kuwa,da zarar ance Mace zatayi
Aure,to ta fara Kiriniya da yawace yawace,itace Gidan Kawaye
da 'yan uwa da Tsofaffin Samarinta da kuma 'Yan Ajinsu[Class
Mates].
Zaka ganta tana wangale baki,musamamn in ka kirata da
sunan AMARYA,ga tsabagen raba Kati da kokarin shirya Kade
kade tun ana da sauran watanni da Biki.
Lokacin da akazo bikin kuwa,wayyo Allah kai kace Mazari ce
saboda RAWA da JUYI har da TSALLE.
Itace zata bi duk wanda ya santa wajen raba musu Katin
gayyata,koma tazo cikin Fcbk,ko Twitter ko Instagram ko
Google+ ko 2Go tana bada sanarwar Bikinta.
Da wahala kaga tana wani kuka koda kuwa garin ne za'a bari
da ita.
Wani juyin ma a daren farko komai yana iya faruwa ba tare da
wani inda inda ba.
Babu Mamaki don fahimtar hakan kaga a cikin watanni 10 an
sami Kazantar DAKI.
Dukkan wan nan bayanin nawa waje daya ne ya dosa kam:
A= Me yasa Matan yanzu basa jin kunya in ance za'ayi Bikinsu
kamar nada???
B= Mazan yanzu wace rawa suka taka wajen canja Tunanin
Mata su koma kamar yanda suke a Yanzu????
Note: Abin fa har a Kauyuka haka yake a yanzu,hatta wa'yanda
basuyi karatun Boko ba babu banbanci da masu karatun!!!

Comments
Post a Comment