TALAKAN AREWA YA WAYE!

TALAKAN AREWA YA WAYE!

Na dade ina jinjina wannan al'amari wlh, ganin yadda talaka ya waye lokaci guda, A jahar Kano 'yan adawa sunriqe wani abu wanda suke tunanin dashine xasu kai gwamnatin Jaar Hula qasa, Wato batun Ruguzau, A Zance na gaskiya gwamnatin jahar Kano tayi rusau dayawa kuma akwai wadanda aka rushewa gidaje batare da anbiyasu diyya ba, haka kuma akwai wadanda aka qwacewa filaye da gonakai, kawai dai idan abin baishafekaba to bazakasan da hakan ba.

'Yan adawa sunyi ta yamadidi da hakan ta yanda har sukan xiyarci wadanda abin yashafa suyi hira dasu domin duniya taji, To amma duk da hakan sai abubuwa sukaqi tafiya dai - dai da yadda 'yan adawar sukaso.

Idan kaduba abinda ke faruwa ma a jahar Kaduna abin xai baka mamaki idan kaji sunan da mutanen jahar ke kiran Nasir El Rufa'i dashi, wato sukance SAI MAI RUSAU wato lokacin da yariqe ministan babban birnin kasar nan yayi qaurin suna wajen rushe gidajen da suka wanzu ba bisa Qa'ida ba.

Kenan duk da ruguzau da rusau din Elrufa'in mutanen jahar ta Kaduna sun yarda kuma sunji sungani, Ma'iya cewa Talakan Nigeria ya waye, Talakan Nigeria cigaban kasarsa kawai yake buqata, Yadena yarda da kururuwar Maqaryata da Mayaudara.

Shin menene silar wayewar Kan Talaka a Nigeria???

Idan nace kashe - kashen al'ummar Musulmai da akaringayi da sunan boko haram yataimaka matuqa gaya wajen wayar da kan talakan Nigeria, ta yanda ya jajurce wajen kawo canji ta dole, ankashe mutane ba adadi a Arewancin nigeria duk wai da sunan boko haram.

Wuya Mai Sa Hadin Kan Dole..!

Ina roqon Allah yakawo Wuyar da zatasa Qungiyoyin musulmai ma suhade kawunansu ta dole! Ace yau ga wata rana taxo an mance da cewa ni Dan qungiya kazane! Sai dai muji ana cewa NI MUSULMI ne kawai! Kuma Musulmi Dan Uwan Musulmi ne, Amma ayadda ake yanxu Dan Qungiya kaza ba dan uwan Dan Qungiya kaza bane! Kowa Dan Qungiyarsa shine Dan Uwansa.

Allah yakyauta!

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA