SAURAYI YAFI BUDURWA SANIN KAN TSIYA

Wani saurayi ne yabi wata budurwa akan hanya

yace mata yana sonta ai saurayin nan bai

yi aune ba sai yaji budurwar nan ta sharareshi da mari a fuska har

sai da marin yayi qara mai qarfin da yasa duk mutanen kewayen

wurin suka ji duk suka waigo da sauri inda suka ji qarar, amma

wuf sai saurayin nan ya 'Daga tafin hannunsa sama kamar shine

ya mari budurwar sannan ya 'Daga muryarsa da qarfi yadda duk

mutanen zasu ji yace wa budurwar "idan kika sake bude baki kika

qara cewa kina sona sai na sake gaura maki mari

fiye da wanda nayi maki yanzu"

Sai duk mutanen wurin suka kalli budurwar nan suka fashe mata

da dariya har suna nunata suna cewa "ihu,

yarinya lalle kinsha mari akan soyayya"

Sai budurwar ta dubi mutanen wurin tace
"Wallahi qarya fa ya

keyi, nine fa na mareshi ba shi ya mareni ba"

Amma mutane ba wanda ko ya kulata, kowa sai dariya yake ta

mata kuma ana ba saurayin hakuri akan ya tafi ya kyaleta

hakanan don kada ya sake marinta, da-kyar aka

Lalla6i saurayin ya hakura ya tafi.

Ita kuwa budurwar sai ta fashe da kuka tana fadin

"Allah Ya Isa sharrin da kayi mun"

Haka mutane suka watse suna ta yin mata dariya

suka barta anan tana ta faman rusa kuka.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA