MIJI NA GARI TAKE SO KO MAI KUDI ?

Watarana wata buduwarwa tana son ta
auri miji nagari sai ta
tafi gurin wani malami ta ce a roka mata
Allah ya bata miji
nagari malamin ya ce to.
Bayan kwana biyu sai buduwar ta koma
wurin malamin ta ce
malam ana addu'ar kuwa, har yanzu shiru
fa?
Malamin ya ce mata ana yi mana har yanzu
ba wanda ya zo
ne? Sai budurwa ta ce eh babu amma
akwai wani dan acaba
ya zo amma ba mu daidai ta ba.
Malam ya ce to ba komai za'a cigaba da
addu'a.
Bayan kamar mako biyu sai budurwar nan
ta koma wajen
malam ta ce ita fa har yau ba biyan bukata
sai malam ya ce
mata ya aka yi kuma sai ta ce, to yanzu
kuma wani ne ya zo a
keke amma na koreshi.
Sai malam ya ce wai wani irin miji kike so
ne?
Budurwa ta ce kamar mai gida da mota da
kudi haka, kuma
dan binni. Daga nan sai malam ya ce ke
tashi bani wuri da munufuncinki idan har
addu'a kike so ake miki to ki fito
ki ce Allah ka bani miji mai kudi, ba ki tsaya
kina noke-noke
ba,. Mu nan idan har addu'ar miji nagari
kike so to wlh in aka
matsa a kafa zaki ganshi ya zo.
Daga nan sai malamin nan ya cigaba da
masifa, aikin banza
aikin wofi matan yanzu duk sun lalace
kowa sai mai kudi
kuma sun fake da wai miji nagari.
YA ALLAH KA BAMU MATA NAGARI WANDA
ZASU SO MU BADON DUKIYAR MU SAI DON
KAI DA KUMA KAUNAR MU RAYA SUNNAR
MANZON KA,,

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA