Kariya Daga Illolin Kayan Kwalliyar Mata

Ko kin san akwai guba iri-iri a kayan kwalliya irin su
jan-baki da hoda da sabulai da man shampoo da na
kwaile fata kuwa? Guba irin wacce ake cewa sai ta
taru da yawa a jini kafin ta iya kawo matsala.

Misali, jan-baki an tabbatar yana da gubar dalma ta
lead wadda ba ta illa farat daya sai an yi ta amfani
da jan-bakin na tsawon shekaru gubar ta taru a jini
kafin ta kawo matsala a lakar jijiyoyin motsi. Shi
kuma man kwaye fata na bilichin zai iya kunsar
gubar mercury mai sa kansar fata da ta jini da
mutuwar koda idan aka dade ana amfani da su.

Masana suka ce wadannan guba sukan shiga jiki ne
ta kofofin fata, wasu kuma kamar na jan-baki lashe
su ake su shiga baki a hadiye, wasu kuma kamar na
kwalliyar ido ta kofofin fatar kasan idon suke shiga.

Akwai wadanda za su ga sun sayi man shafawa ko
kayan shafe-shafe masu kunshe da irin wadannan
guba sun yi amfani da shi, sun ga bai musu ba, wato
ko dai ya kawo kaikayin fata ko kuraje ko kumburin
fatar ko ma jikin gaba-daya. Akwai kuma wadanda
ba sa jin wasu alamu. Kumburin jiki gaba-daya shi
ne aka fi gani musamman a masu amfani da man
bilicin. Wannan kumburi na nufin koda ta fara
tabuwa ke nan. Yawancinsu da sun bari cikin lokaci
kodar ke dawowa, kumburin ya sacce, wadanda ba
su bari cikin lokaci ba kuma, zai iya kashe musu
koda gaba daya.

Wasu masana a Jami’ar Fatakwal da suka bincike
samfurin kayan shafe-shafe a kasuwannin kasar nan
sun tabbatar da cewa ana sa gubar dalma da ta
mercury da ire-irensu fiye da kima a kayan shafar.
Suka kara da cewa alhakin Hukumar NAFDAC mai
kula da abinci da magunguna da Hukumar SON mai
kula da shige-da-ficen kayan amfanin yau-da-kullum
idan suna bari ana shigo mana da irin wadannan
kayan.

A daidaikunmu ba abin da za mu iya yi face mu rage
yawan kwalliyar shafe-shafe, wato yau a yi, gobe a
bari misali. A kuma rika duba abubuwan da aka
rubuta na kunshe a cikin wadannan kayan shafe-
shafe kafin mu saya. Akwai wurin da akan rubuta
‘ingredients’ a jikin kwalbar kowane kayan shafa. A
nan ne ya kamata a gani idan akwai guba irin su
lead da mercury (wanda akan rubuta mercury, ko
Hg, mercuric iodide, mercurous chloride,
ammoniated mercury, amide chloride of mercury,
kuicksilber), da formaldehyde, da ma dai duk wani
sinadari da mace ke da shakku a kai. Idan akwai su
a ciki, kada a saya.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA