JATAU NA KYALLU

ADABI: Nazari A Kan Littafin Jatau Na Kyallu

Darussan Littafin A Mizanin Rayuwa.
•Sunan Littafi: Jatau Na Kyallu Wallafar Madabba’ar NNPC, An maimaita bugunsa tun daga shekarun 1970 Zuwa 1974 da 1976 da 1978 da 1980 ,da 1981 da 2011 da 2004 da kuma 2006 da 2008 da 2010.
Wannan littafin ya yi suna a zamaninsa ,sai dai ni a wajena har zuwa yanzu littafi ne mai cin zamanin zamunna wato yana kunshe da darasin rayuwa mai matukar amfani, a ko yaushe mutum ya karanta zai karu, musamman ga mutane masu hangen nesa.

Wannan littafin da aka rubuta a fasalin wasan kwaikwayo ya kunshi wasu siffofi masu hasko rayuwa ta zahiri mai Kamanceceniya da rayuwar yau da kullum ta wasu mutane.

Mallam Jatau wani hamshakin mutun ne dan kasuwa kuma kamar malami, a gefe guda kuma bin duniya ya ke yana sheke ayarsa a bariki. Duk da cewa yana da matansa hudu na aure da kuyangun da ya gada wajen kakansa, to a bayan fage kuma ga karuwarsa Madan Jiniya wacce daga baya ta koma Kyallu, wacce a lokacin tana kan ganiyarta, ‘yan birni na barin kudi a kanta, manyan attajirai na yayinta suna yi mata hidima har ta kai dai manya ne kawai ke iya zuwa wajenta, ta fi karfin kananan ‘yan bariki. A wannan yanayi kuwa Jatau ya fara tunanin auren madam Jiniya ya kawo gidansa. A ganinsa wannan shi ne cinyewa da burgewa da kuma munanawa sauran attajirai cewa fa shi ya tserewa sa’a . Nan da nan kuwa ya kori matarsa guda daya cikin matansa hudu, ya auro madam Jiniya wacce ta shafe shekaru a fagen bariki, bayan auren ta sauya suna ta koma Kyallu daga Madam Jiniya.

Bayan kasancewar auren Jatau da Kyallu, Jatau ya yi tsammanin shiryuwa za ta samu Kyallu har yake ce mata, “Yanzu Kyallu kin ga shiryuwar ubangiji da rahmansa ya same ki, kin yi aure, abin da a ke son dukka diya mace ta yi. Ba ki sanin mutane da yawa tun da ba irin wadanda muka yi Karon Batta a gidan ki ba , sai wani zancen banza suke yi, wai yaudara ce kawai wai ba za ki zauna a gidan nan ba. Domin Allah ki dubi kamar Yamanin wanda ba mu rabuwa da shi, mutumin da kika fara saninmu tare, wallahi don ki sani bama ko ga muciji tsakaninmu da shi. Kamar yadda musulmi ba ya san, kafiri, haka ba ya son ko hanya ta gama mu da shi. Don mallam yautai kuwa mutumin da ya ke ni ne na ba shi bashi, da har ake lissafinsa ,cikin masu arzikin kasannan ,wai shi ne, cikin ‘yan iska masu kulla mini sharri da jam-hurun tsiya. Saura bai kome ,ma gamu da ko wannensu da dai –dai da dai-dai. Bariki ba gayya bace kowa da kafarsa ya zo. Da ikon Allah sai na ga bayansa. Zamanmu da ke kuwa, wanda ba su so zai dore ne, mu ba mara da kunya…”

Ita kuwa Kyallu da boyayyiyar manufarta a zuci, ta san fa cewa Jatau ya yi mata daukan kara da kiyashi, ko kuwa kallon kitse a rogo, domin a nata bangaren kwadayin dukiyarsa ne kawai ya kaita ga aurensa ba wai don tana kaunarsa ba.

Har ila yau kuma ba ta zabe shi a matsayin masoyinta ba, kwadayin dukiya da kadara ne kawai ya sanya ta amince ta aure shi, kuma tana zaune a gidansa ne amma zuciyarta na bariki, ganin cewa shi bai fahimci ina ta dosa ba sai ta ci gaba da yi masa lumbu-lumbu, kasancewarta mage mai kwanciyar daukar rai sai ta ci gaba da shimfida masa kalmomin yaudara inda a shafi na daya kashi ba daya, ta ce da shi: “In Allah Ubangiji ya shiryi mutum da shiriyarsa ai shike nan ba sai gafalallu su je su ci gaba da gafalarsu ba. Ni me zan cewa Allah, ban da in kara gode masa! Kai kuma in kara gode maka. Ga shi har yau ni ce a ke kira da sunan yanka, Kyallu! Da kamar can ne da ba wata tsiya ba ce wai ita Madam Jiniya, za a kira ni da ita ba! Allah na tuba ka gafarce ni da na kira wannan mummunan suna da bakina. Allah ka kara taimakonmu da taka tudun mun tsira amin….

Haka dai Kyallu ta yi ta kara mallake zuciyar Jatau da kalamai masu dadi, har ta kai ya juyawa sauran matansa baya, ba ya iya sauraron maganar ko waccen su sai abin da Kyallu ta shirya masa, ta dinga shirya masa makirci da kisisina tana karbe masa dukiya cikin dabarunta dai tuni ta raba shi da cin abincin sauran matan, da safe ba sa cin dumamen tuwo sai shayi da biredi, sannan ga wanki da guga da a ke yi musu, sai dai ta yi masa lissafi ya kirga kudi ya bata ta boye.

Tun kafin auren Kyallu dai Jatau ya gagari matansa ba ya iya zama a gida bare ya kiyaye hakkokinsu, in ya fita daga gida da magariba ba ya komawa gidan sai kusan asuba, matan sun kai kara wajen iyaye da ‘yan’uwa sun gaji kuma maimakon a samu sauki da ya auro ta, sai kuma ya sake canja wani salon na zaman dakin Kyallun, in magariba ta rufa ya shige cikin dakin ba ya sake fitowa sai gari ya waye, nan kuma kishi ya addabe su, lamarin na ci wa matan Jatau tuwo a kwarya, yadda Kyallu ta mamaye zuciyar mijinsu har ya kai baya iya yi musu adalci a tsakani.

Sannan sun lura duk ranar girkinsu ba ya iya zama a gida ya ba su hakkinsu. Cikin wani dare, ranar girkin Kyallu sun shige daki ita da Jatau, Biyu daga cikin matansa su ka hadu suna tattaunawa a kan halin da suke ciki, uwargida ta ce, “Rabu da su ‘ya’yan bado. Tun dazun na ke jinsu suna ta yin abu daya. Munafuka in bai yi hankali ba sai ya dauko abin da zai hallaka shi da kudinsa ne bai sani ba. ‘Yan nan idan kika daka ta wadannan marasa kunyar ko rintsawa ba za ki yi ba, sai ki yi ta lilo cikin tsakar gidan nan, har garin Allah ya waye miki, ba ki rintsa ba.

Baranya ta ce, “Idan haka kuwa abin zai zama, yaya ni kam zamana a cikin gidan nan ya kare kenan. Ke kin saba, ba zan yarda ina karamata, haka a tsofad da ni ba kawai… Allah ya isa!”

Haka matan Jatau su ka yi ta korafe-korafe a tsakaninsu, tare da jin ciwon yadda madam Jiniya ta kwace musu muji, ta mayar da su rigar bayan Sallah.

Ita kuwa Kyallu Allah ya kashe ya bata mushe a mahauta, yadda ta so haka ta ke juya Jatau, har ta da kasuwancinsa ma ta shiga ciki don buhunhunan shinkafa a ke siyo mata tana siyarwa, masu motocin Jatau ke dakko mata in za su kawo kaya wanda duk ya kuskura bai dauuko shinkafar Kyallu ba sai ta saka Jatau ya kore shi.

Daga baya da ta fahimci ta gama da shi ta mallake shi sai ta sake fito da sabuwar hanyar cin kudi a saukake, inda ta kwanta laulayin ciwon karya, ta tayar da hankalin Jatau ya kasa zaune ya kasa tsaye, ita kuwa tace a kiran yo mata kawarta ta bariki wato Shamuwa, a cewarta ita ce kawai ta san gidan malamin da zai bayar da makarin ciwon nata. Daman tuni ta shirya makircin cewa tana da ciki tun da ta san abin da Jatau ke son ya ji labari kenan sannan tace ita wannan lalurar kuma ke sanya cikin ya zube.

Jatau ya kirawo Shamuwa ya dunkule makudan kudi masu yace ta karbo mata maganin ko ta samu lafiya.

Yana fita suka yi shewa su ka tafa, sannun suka bude babin hirarsu ta ‘yan bariki da karuwai, inda Kyallu ta yi ta tambayar labarin samarinta da kuma tambayar shin wacce waina a ke toyawa a bariki.

Hira ta ci gaba da gudana a tsakaninsu inda a shafi na goma sha day, kashi na uku, Shamuwa ta ke cewa Kyallu, “Ga malamin naki kuwa bai iya dariya ba, kamar wanda ya ga wawan zama. Yanzu kuwa don Allah ya gane wayonki?

Kyallu ta ce “Ya gane! In ya gane; ashe yana da hankali kenan, wauta kuma ta ci me? Wannan mahaukacin da ki ke gani nice zan kara karya shi. Ba ma zakara bane zai ba shi sa’a ba, yara ne za su kara tura shi, in ya fara sambatun karewar kudi domin kafin hudowar kakan nan sai na yi masa kaca-kaca, na bar shi tantirinsa, kamar farkon zuwansa garin nan. Gida da motar haya kamar na same su a jikinsa na gama. Rabu da shi ba wai na ji bana za shi Hajji ba, ai sai ya canza sunansa ya sa nawa…

Haka kuwa Kyallu ta ci gaba da Burma Jatau tana kwace masa dukiya tana boyewa. Sauran abokanan zamanta kuwa sai ta dinga kulla musu makircin, zagon kasa iri-iri, tace wannan tace wancan, musamman a kan irin girkin gida, sai ta dinga cewa Jatau duk kayan miyar da yake kawowa gidan matansa sayarwa su ke yi, in kuwa ba su siyar ba sai su kaiwa abokanan su a makota, su yi miyarsu haka ba dadi don haka dole Jatau ke ba ta kudin abinci ta sayi wanda ranta ke so.

Su kuwa abokan Jatau da makwabtansa tuni girmansa ya fadi a idanunsu duk inda suka zauna hira su kan tattauna a kan sakarcinsa na auren karuwa. A fita ta biyu, shafi na goma sha biyu. Jamanu da su Jarmai da Malam Yautai suka zauna hira; Jamanu yace “Ana gafala a duniya nan! Kun san abin da ke tsakaninmu da M. Jatau gafalallen banza? Wai yanzu shi ne Ubangijin shigewa ta gidana, yana wannan irin taka kasa gab, gab, irin ta su, ‘Karfin banza’ Ganinsa wai, kamar ya yi wani abin a zo agani ne, da wani ba zai iya ba, domin auren sakaran nan Madam Jiniya, gwangwanin bariki, karyar giya (su yi dariya).

Shi kuwa Jarmai yace, “A’a, haba Jamanu, ai ko ya sha giyar wake ba zai fara yi maka haka ba. Shi M. Jatau din, mantawa ya yi? In kuma bai sani ba a cikin masoyansa a rasa wanda zai tsegunta masa ne, a lokacin da ta zo ganin gida irin kirbin arzikin da kuka yi da ita? Ashe ba kaine ka ce mata ta koma gidan mujinta haka ba? Sau nawa yana aikowa yana magana da ita cikin tarho, yana aiko mata da waya? Yaronsa dai-dai sau tara yana zuwa su tafi tana ki, zancen banza, kwace Madam Jiniya a wurinsa, in ana so wani abu ne…!

Malam Yautai kuwa cewa ya yi “Rabu da shi kana tsammanin mahaukacin yana da wayon sanin haka ne? Ni ma, ba ga ‘yan jarin da ya ke ba ni saboda ganin muna yawo da kai, ya hana ni kemagadas? Ga wata haukar da duk mutumin da ya ji sai ransa ya baci. Ya kori matar yaronsa Danmaikosai, wai don bata zuwa da safe tana gaida Kyallu.

Suka fashe da dariya) Yau ga gafala mai ya hada matarsa da matar yaronsa…?

Da yawan mutane dai kallon Wawa kanin mahaukaci su ke yiwa Malam Jatau da ya kasa ganewa cewa auren Kyallu fa ba burgewa ba ne, sakarci ne kawai da shashanci musamman yadda ya kasa gane irin makirci da kisisinarta

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA