HUKUNCE-HUKUNCEN ALWALA
HUKUNCE-HUKUNCEN ALWALA
Gabatarwa: Alwala ibadace mai zaman
kanta wacce Allah madaukakin sarki ya
sahar'antata kafin gabatar da wadansu
ibadu musammamma sallah, mutum yana
samun cikakken ladan alwala idan ya yi ta
cikakkiya, Allah madaukakin sarki ya
saukar da hukunce-hukuncen alwala a
cikin littafinsa mai girma alkur'ani:
'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi
imani, idan kuka ta shi za ku yi sallah
to ku wanke fuskokinku da
hannayanku zuwa gwiwar hannu ku
kuma shafa kawunanku da kafafanku
zuwa idan sawu (idan kafa)…'' Suratu
Ma'ida, aya ta:6.
Tabbas wannan aya ta ti bayanin wajibcin
alwala lokacin da za'a yi sallah, kuma ta
bayyana gabban da ya zama wajibi
anwanke ko kuma anshafa, sannan kuma
ayar ta iya kance ko wanne mahalli,
sannan kuma Ma'aikin Allah –Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi- ya
bayyana siffar yadda alwalar take da
maganarsa da kuma aikinsa bayanin da
yake gamsasshan bayani.
Ka sani lalle ita wannan alwala tanada
falala da kuma sharudda da kuma farillai
sannan tana da sunnoni da kuma
mustahabbai, sharuddannan da farillai
tabbas a tabbata ansame alokacin gabatar
da alwala iya gwargwado domin da sune
alwala zata zama karbabbiya, amma su
sunnoni da mustahabbai suna cika
alwalarne ta inda matsayinsu bai kai
matsayin sharuddai da farillaiba.
Falalar Alwala: Dudda cewa alwala
wajibice wannan kadai ya isheta samun
matsayi a musulunci domin dukkan abinda
akace farillane to wannan matsayi ne me
zaman kansa, bayan hadisi na 62 a cikin
Muwadda'u Malik yana cewa: '' An karbo
daga Abdullahi As-Sunaabihi, lalle
ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi yace:
''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya
yi kuskurar baki dukkanin laifukan
dake bakin sun fice, idan kuma ya face
laifukan (Day a shaka) sun fice, to idan
kuma ya wanke fuskarsa laifukan da ke
fuskar ta sa sun fice, har wadanda ke
karkashi girar shi, idan ya wanke
hannayansa laifukan dake hannayansa
sun fice, har wadanda ke karkashi
faratansa (jam'in farce), to idan kuma
ya shafi kanshi laifukan dake kan nashi
sun fice har wadandake kunnuwansa,
to idan kuma ya wanke kafafuwansa
duk laifukan dake kafafuwan nasa sun
fice, har wadanda ke karkashi farcen
kafafun nashi. Sannan kuma tafiyar da
ya yi zuwa masallaci ya zama wani
karine da yake da shi''.
Lalle wannan bakamar falala bace da
alwala take da shi, domin mai alwala zai
kasance yana kammala alwala zunubanshi
suna digewa a kasa, amma gudu ba
hanzariba wannan ladan zai tabbata ne ga
wanda ya yi alwala da shara'a ta tabbatar
da ita ba wacce ya tsinta a kan titi ba.
Sharuddan Alwala: Sharuddan alwala
sune abubuwan da ake so mai alwala ya
cika su kafin ya fara alwalar, sune kamar
haka:
(1) Musulunci, kenan idan wanda ba
musulmiba ya yi alwala bata yi ba.
(2) Hankali, idan mahaukaci ya yi alwala
itama bata yi ba.
(3) Wayau, idan dan karamin yaro mara
dabara ya yi bata yi ba.
(4) Ruwan ya zama mai tsarki, idan ya
zama ruwane mara tsarki to alwalar bata
yi, bayanai sun gabata akan hukunce-
hukuncen ruwa.
(5) Ruwan ya zama na halas, idan
ruwane da mutum ya sata ko ya same shi
bata shar'an tacciyar hanyaba to alwalar
bata yi ba.
(6) Ya kasance mai tsarki, idan mai
alwala ya kasance ya yi fitsari ko bayan
gida misali wato ya kasance mara tsarki
kafin alwala to ko ya yi alwalar bata yi ba.
(7) Gusar da duk abinda zai hana ruwa
shiga, kenan idan mutum ya kasance
yaba sanye da wani abunda zai hana ruwa
ya kai ga fatar jiki to dolene ya cire shi,
kamar tabo (laka)…'.
Farillan Alwala:
(1) Niyyah: Domin a banbance wanda ya
sa ruwa donin sanyaya jiki, ko domin
gusar da datti, duk wannan ba niyyace ta
alwalaba.
(2) Wanke Fuska: ita kuma fuska ta
bangaren tsawo tana farawane daga
matsirar gashin kai (banda sanko) zuwa
karshen mukamiki, amma ta fuskar fadi
tana farawane daga kunnan dama zuwa
kunnan hagu, wannan shine abinda yake
amsa fuska, kenan dole mai alwala ya
tabbatar ko ina ya sami ruwa kamar kasan
haba, gefan ido da gefan kunne da matsa-
matsin karan hanci, ayi hattara sosai
domin wasu alwalarsu kamar alwalar
yarace.
(3) Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar
Hannu. Mai alwala mace ko namiji ya
tabbata ya wanke hannayansa tun daga
saman yatsunsa (farce-akaifa) harzuwa
gwiwar hannu ya tabbata gwiwar ta shiga
inda ya wanke, anamma akwai manya
masu alwalar yara.
(4) Shafar Kai: Ka tabbata ka hada
yatsunka sannan kuma ka fara shafar
daga goshi (daidai matsirar gashi) sannan
ka shafa zuwa keya.
(5) Wanke Kafa: Hakanan mai alwala ya
tabbata ya wanke kafarsa harzuwa idon
sawu, wato wadannan kasusuwan guba
biyu dake gefan kafafuwa sun shiga cikin
inda aka wanke.
(6) Cudanyawa: Mai alwala ya tabbata ya
cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa
ya shiga ko ina.
(7) Yinsu Baidaya: Abinda ake nufi shine
alokacin da ka fara alwala to ka dakatar
da komai sai ka kammala, amma kana
alwala kana kuma wata sabga daban
wannan bai yi ba.
Mai alwala ya tabbata ya gabatar da
wadannan ayyuka a lokacin da yake
alwala ta yadda idan aka rasa daya daga
cikin su to alwalarsa ta shiga hadari.
Sinnonin Alwala:
(1) Wanke Hannaye Kafin A Tsoma Su A
Ruwa. Ta yadda mai alwala zai karkato
butar alwala domin ya wanke hannayansa
zuwa Ku'u wato wuyan hannu.
(2) Kuskurar Baki: mai alwala ya tabbata
ya sanya ruwa a bakinsa sannan kuma ya
kada ruwan a baki, wannan shi ake kira da
kuskurar baki.
(3) Shaka Ruwa: Shine mai alwala ya
shaki ruwa ruwan ya shiga hancin sa sosai,
sai dai kawai idan yana azumine sai yayi
kadan. Amma yadda mutane suke shafar
hancinsu wai da sunan shaka ruwa
wannan baiba.
(4) Facewa: mai alwala zai shaki ruwanne
da hannun dama sai ya sa hannun haku
akan karan hancinsa, sannan sai ya fyato
ruwan da ya shaka.
(5) Shafar Kunne; Mai alwala ya tabbata
ya shafi cikin kunnensa da wajan kunnan,
zaka/ki sanya yatsanka 'yar-manuniya a
cikin kunnan sannan ka babban yatsa a
wajan kunnan sannan sai ka shafa,
Dirkashi!.
(6) Sake Taba Ruwa: Alokacin da zaka
shafi kunne shin zaka shafi kunnanne da
ragowar danshin hannuka da ka yi shafar
kai da shi? Ko ko zaka sake taba ruwa na
musamman domin shafar kunne, malamai
sun karawa juna san, ko wanne ka yi ya yi
daidai.
(7) Dawo Da Shafar Kai: Ka tsaya ka
fahimta, ita shafar kai farillace, amma
dawo da shafar kai sunnace daga cikin
sonnonin alwala.
(8) Jeranto Farillai: Ta yadda zaka
kawosu daya-bayan-daka kamar yadda
aka lissafosu, kada ka dauki na uku ya
zama shine na farko sannan ka biyo shi
dana biyar, misali…'.
Wadannan matsayisu bai kai matsayin
farillaiba, amma suna cikin manyan
abubuwan da suke cika alwala.
Mustahabban Alwala:
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni,
kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi,
wadanda suke dukansu biyun farillai na
gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko
mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su,
domin kowannanmu so yake ya yi ibada
cikakkiya kammalalliya, to ko tunda
hakane bai kamata yace ai wannan
mustahabbine ya daukeshi kamar wani
kankanin abu.
Su mustahabban alwala suna da yawa,
amma yanzu ga kadan daga cikinsu:
(1) Anbaton Allah yace ''Bismillah'',
adaidai loakcin da zaka fara alwala, amma
idan mutum ya manta saida yake tsakiyar
alwalar ya tuna bakomai sai ya yi a
lokacin.
(2) Addu'a bayan kammala alwala, itace
kuma kamar haka:
ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ،
ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﺟﻌﻠﻨﻲ
ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻮﺍﺑﻴﻦ، ﻭﺍﺟﻌﻠﻨﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺘﻄﻬﺮﻳﻦ.
Ma'ana: ''Ina shaidawa da babu
abinbauta da cancanta sai Allah, kuma
shi kadai yake bashi da abokin tarayya,
kuma ina shaidawa lalle (Annabi)
Muhammad bawan Allah ne kuma
manzansa ne, Ya Allah ! ka sanya ni
daga cikin masu yawan tuba, kuma ka
sanya ni daga masu neman tsarkaka.''
(3) Karanta Ruwa: Bawai ana nufin mai
alwala ya shasshafa gabbansa bane, a'a,
ana bukatar ya yi anfani da ruwa amma
kada ya malalar da shi, domin yana daga
cikin tsarin musulunci tattali da tsimi da
tanadi.
(4) Gabatar Da Asuwaki: Bayani kuma
dama ya gabata akan asuwaki, ana yi da
danye ko da busasshe, idan bai samuba
sai ayi da yatsa, amma mu sani asuwaki
daban kuskurar baki ma daban. Hakanan
kuma ko da mutum lokacin sallah ya yi
kuma amma yana da alwala to abinda ake
so shine ya yi asuwaki.
(5) Wuri Mai Tsarki: An so inda zaka yi
alwala ya zama wurine mai tsarki.
(6) Dama Kafin Hagu: abin nufi shine ka
fara wanke hannun dama kafin hannun
hagu, hakanan ka fara wanke kafar hagu
kafin ta dama.
( 7) Jerantawa: Wato jeranta kowacce
sunnah tare da 'yar-uwarta, kamar fara
gabatar da kuskurar baki kafin shaka
ruwa.
(8) Wankewa Sau Uku: Ma'ana wanke
wuraran da ake wankewa sau uku, mu
sani wankewa sau uku zai zama
mustahabbine idain wankewar farko ta
game ko ina, amma idan ta farko bata
gamaba to ta biyu tananan amatsayin
wajibi, haka namma idan ta biyun idan bat
agama ba to ta uku tana nan a matsayin
wajibi. Ya zama wajibi mai alwala mace ko
namiji ya kula sosai ya cuccuda inda ya
kamata ya sa ruwa ba tare da barnaba.
Amma shi kais au daya ake shafarsa, ba'a
shafar kai sau uku. Sannan kuma mutum
ya tabbata a wadannan wankewa da
akace ya yi sau uku bai kara akan hakan
ba, ya yi iya kokarinsa ya ga guda ukun
sun kammala.
Wadannan kadan kenan daga cikin
mustahabban alwala, kuma wadannan
bayanai sun mata kamar yadda suka shafi
maza, sai dai mata su sani gashin kansu
da sangalin hannuwansu duka al'aurane,
saboda haka bai halatta su bayyanar da su
ga maza, ken an idan zaki yi alwala sai ki
sami wuri ki kawwame kanki.
Wadannan bayanai da suka gabata zasu
haskaka mana yadda alwala take, amma
hanya mafi sauki shi ne a yi maka ita a
aikace ka gani domin haka sahabban
ma'aikin Allah suka yi, an tambayi Usman
dan Affan dan gane da alwala sai yasa aka
kawo mishi butar alawala ya yi musu ita a
aikace, yace kuma irinta ma'aikin Allah ce.
Anan nake kira ga dukkanin limamai na
juma'a dana sauran masallatai da kuma
malamai a jami'oi da kwalejin ilimi da
kuma malamai a sakandare da firamare
da malaman islamiyyu da malamai masu
karantarwa a masallatai da masu wa'azi
da sauran wadanda abin ya shafa da su
karantar da mutane ita wannan alwalar a
aikace kowa ya gani ya kuma yi tambaya,
kada ka ga kamar kowa ya gane da zarar
ka yi ta a aikace zaka ga abin mamaki, ni
na taba gwada hakan, ita ibada sai an
koyawa mutum ba wai daka kawai
shikenan ya iyaba, ko kuma ai shi iyaye da
kakanni duk musulmai ne sabo da haka ba
sai ya koyaba, duk wannan maganace ta
wanda yake nesa da makaranta, kai da
ganin alwalar wani kasan bai je
makaranta ba, Allah ya karba mana
ibadummu.
Kammalawa: Lalle wadannan bayanai
sun kara tabbatar mana ashe alwa abace
da sai an tashi tuku domin a koyeta tana
da falala da kuma sharudda sannan ga
farillai da sunnoni da kuma mustahabbai,
lalle ka nana bukatar malamai daga
kowanne bangare su tashi tsaye su
karantar da al'umma wannan ibada a
aikace, domin a gudu tare a tsira tare.
Gabatarwa: Alwala ibadace mai zaman
kanta wacce Allah madaukakin sarki ya
sahar'antata kafin gabatar da wadansu
ibadu musammamma sallah, mutum yana
samun cikakken ladan alwala idan ya yi ta
cikakkiya, Allah madaukakin sarki ya
saukar da hukunce-hukuncen alwala a
cikin littafinsa mai girma alkur'ani:
'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi
imani, idan kuka ta shi za ku yi sallah
to ku wanke fuskokinku da
hannayanku zuwa gwiwar hannu ku
kuma shafa kawunanku da kafafanku
zuwa idan sawu (idan kafa)…'' Suratu
Ma'ida, aya ta:6.
Tabbas wannan aya ta ti bayanin wajibcin
alwala lokacin da za'a yi sallah, kuma ta
bayyana gabban da ya zama wajibi
anwanke ko kuma anshafa, sannan kuma
ayar ta iya kance ko wanne mahalli,
sannan kuma Ma'aikin Allah –Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi- ya
bayyana siffar yadda alwalar take da
maganarsa da kuma aikinsa bayanin da
yake gamsasshan bayani.
Ka sani lalle ita wannan alwala tanada
falala da kuma sharudda da kuma farillai
sannan tana da sunnoni da kuma
mustahabbai, sharuddannan da farillai
tabbas a tabbata ansame alokacin gabatar
da alwala iya gwargwado domin da sune
alwala zata zama karbabbiya, amma su
sunnoni da mustahabbai suna cika
alwalarne ta inda matsayinsu bai kai
matsayin sharuddai da farillaiba.
Falalar Alwala: Dudda cewa alwala
wajibice wannan kadai ya isheta samun
matsayi a musulunci domin dukkan abinda
akace farillane to wannan matsayi ne me
zaman kansa, bayan hadisi na 62 a cikin
Muwadda'u Malik yana cewa: '' An karbo
daga Abdullahi As-Sunaabihi, lalle
ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su
tabbata agareshi yace:
''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya
yi kuskurar baki dukkanin laifukan
dake bakin sun fice, idan kuma ya face
laifukan (Day a shaka) sun fice, to idan
kuma ya wanke fuskarsa laifukan da ke
fuskar ta sa sun fice, har wadanda ke
karkashi girar shi, idan ya wanke
hannayansa laifukan dake hannayansa
sun fice, har wadanda ke karkashi
faratansa (jam'in farce), to idan kuma
ya shafi kanshi laifukan dake kan nashi
sun fice har wadandake kunnuwansa,
to idan kuma ya wanke kafafuwansa
duk laifukan dake kafafuwan nasa sun
fice, har wadanda ke karkashi farcen
kafafun nashi. Sannan kuma tafiyar da
ya yi zuwa masallaci ya zama wani
karine da yake da shi''.
Lalle wannan bakamar falala bace da
alwala take da shi, domin mai alwala zai
kasance yana kammala alwala zunubanshi
suna digewa a kasa, amma gudu ba
hanzariba wannan ladan zai tabbata ne ga
wanda ya yi alwala da shara'a ta tabbatar
da ita ba wacce ya tsinta a kan titi ba.
Sharuddan Alwala: Sharuddan alwala
sune abubuwan da ake so mai alwala ya
cika su kafin ya fara alwalar, sune kamar
haka:
(1) Musulunci, kenan idan wanda ba
musulmiba ya yi alwala bata yi ba.
(2) Hankali, idan mahaukaci ya yi alwala
itama bata yi ba.
(3) Wayau, idan dan karamin yaro mara
dabara ya yi bata yi ba.
(4) Ruwan ya zama mai tsarki, idan ya
zama ruwane mara tsarki to alwalar bata
yi, bayanai sun gabata akan hukunce-
hukuncen ruwa.
(5) Ruwan ya zama na halas, idan
ruwane da mutum ya sata ko ya same shi
bata shar'an tacciyar hanyaba to alwalar
bata yi ba.
(6) Ya kasance mai tsarki, idan mai
alwala ya kasance ya yi fitsari ko bayan
gida misali wato ya kasance mara tsarki
kafin alwala to ko ya yi alwalar bata yi ba.
(7) Gusar da duk abinda zai hana ruwa
shiga, kenan idan mutum ya kasance
yaba sanye da wani abunda zai hana ruwa
ya kai ga fatar jiki to dolene ya cire shi,
kamar tabo (laka)…'.
Farillan Alwala:
(1) Niyyah: Domin a banbance wanda ya
sa ruwa donin sanyaya jiki, ko domin
gusar da datti, duk wannan ba niyyace ta
alwalaba.
(2) Wanke Fuska: ita kuma fuska ta
bangaren tsawo tana farawane daga
matsirar gashin kai (banda sanko) zuwa
karshen mukamiki, amma ta fuskar fadi
tana farawane daga kunnan dama zuwa
kunnan hagu, wannan shine abinda yake
amsa fuska, kenan dole mai alwala ya
tabbatar ko ina ya sami ruwa kamar kasan
haba, gefan ido da gefan kunne da matsa-
matsin karan hanci, ayi hattara sosai
domin wasu alwalarsu kamar alwalar
yarace.
(3) Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar
Hannu. Mai alwala mace ko namiji ya
tabbata ya wanke hannayansa tun daga
saman yatsunsa (farce-akaifa) harzuwa
gwiwar hannu ya tabbata gwiwar ta shiga
inda ya wanke, anamma akwai manya
masu alwalar yara.
(4) Shafar Kai: Ka tabbata ka hada
yatsunka sannan kuma ka fara shafar
daga goshi (daidai matsirar gashi) sannan
ka shafa zuwa keya.
(5) Wanke Kafa: Hakanan mai alwala ya
tabbata ya wanke kafarsa harzuwa idon
sawu, wato wadannan kasusuwan guba
biyu dake gefan kafafuwa sun shiga cikin
inda aka wanke.
(6) Cudanyawa: Mai alwala ya tabbata ya
cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa
ya shiga ko ina.
(7) Yinsu Baidaya: Abinda ake nufi shine
alokacin da ka fara alwala to ka dakatar
da komai sai ka kammala, amma kana
alwala kana kuma wata sabga daban
wannan bai yi ba.
Mai alwala ya tabbata ya gabatar da
wadannan ayyuka a lokacin da yake
alwala ta yadda idan aka rasa daya daga
cikin su to alwalarsa ta shiga hadari.
Sinnonin Alwala:
(1) Wanke Hannaye Kafin A Tsoma Su A
Ruwa. Ta yadda mai alwala zai karkato
butar alwala domin ya wanke hannayansa
zuwa Ku'u wato wuyan hannu.
(2) Kuskurar Baki: mai alwala ya tabbata
ya sanya ruwa a bakinsa sannan kuma ya
kada ruwan a baki, wannan shi ake kira da
kuskurar baki.
(3) Shaka Ruwa: Shine mai alwala ya
shaki ruwa ruwan ya shiga hancin sa sosai,
sai dai kawai idan yana azumine sai yayi
kadan. Amma yadda mutane suke shafar
hancinsu wai da sunan shaka ruwa
wannan baiba.
(4) Facewa: mai alwala zai shaki ruwanne
da hannun dama sai ya sa hannun haku
akan karan hancinsa, sannan sai ya fyato
ruwan da ya shaka.
(5) Shafar Kunne; Mai alwala ya tabbata
ya shafi cikin kunnensa da wajan kunnan,
zaka/ki sanya yatsanka 'yar-manuniya a
cikin kunnan sannan ka babban yatsa a
wajan kunnan sannan sai ka shafa,
Dirkashi!.
(6) Sake Taba Ruwa: Alokacin da zaka
shafi kunne shin zaka shafi kunnanne da
ragowar danshin hannuka da ka yi shafar
kai da shi? Ko ko zaka sake taba ruwa na
musamman domin shafar kunne, malamai
sun karawa juna san, ko wanne ka yi ya yi
daidai.
(7) Dawo Da Shafar Kai: Ka tsaya ka
fahimta, ita shafar kai farillace, amma
dawo da shafar kai sunnace daga cikin
sonnonin alwala.
(8) Jeranto Farillai: Ta yadda zaka
kawosu daya-bayan-daka kamar yadda
aka lissafosu, kada ka dauki na uku ya
zama shine na farko sannan ka biyo shi
dana biyar, misali…'.
Wadannan matsayisu bai kai matsayin
farillaiba, amma suna cikin manyan
abubuwan da suke cika alwala.
Mustahabban Alwala:
Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni,
kenan sunnoni sun fi mustahabbai karfi,
wadanda suke dukansu biyun farillai na
gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko
mustahabbai da mutum zai yi sakaci da su,
domin kowannanmu so yake ya yi ibada
cikakkiya kammalalliya, to ko tunda
hakane bai kamata yace ai wannan
mustahabbine ya daukeshi kamar wani
kankanin abu.
Su mustahabban alwala suna da yawa,
amma yanzu ga kadan daga cikinsu:
(1) Anbaton Allah yace ''Bismillah'',
adaidai loakcin da zaka fara alwala, amma
idan mutum ya manta saida yake tsakiyar
alwalar ya tuna bakomai sai ya yi a
lokacin.
(2) Addu'a bayan kammala alwala, itace
kuma kamar haka:
ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺣﺪﻩ ﻻ ﺷﺮﻳﻚ ﻟﻪ،
ﻭﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪﺍ ﻋﺒﺪﻩ ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﺟﻌﻠﻨﻲ
ﻣﻦ ﺍﻟﺘﻮﺍﺑﻴﻦ، ﻭﺍﺟﻌﻠﻨﻲ ﻣﻦ ﺍﻟﻤﺘﻄﻬﺮﻳﻦ.
Ma'ana: ''Ina shaidawa da babu
abinbauta da cancanta sai Allah, kuma
shi kadai yake bashi da abokin tarayya,
kuma ina shaidawa lalle (Annabi)
Muhammad bawan Allah ne kuma
manzansa ne, Ya Allah ! ka sanya ni
daga cikin masu yawan tuba, kuma ka
sanya ni daga masu neman tsarkaka.''
(3) Karanta Ruwa: Bawai ana nufin mai
alwala ya shasshafa gabbansa bane, a'a,
ana bukatar ya yi anfani da ruwa amma
kada ya malalar da shi, domin yana daga
cikin tsarin musulunci tattali da tsimi da
tanadi.
(4) Gabatar Da Asuwaki: Bayani kuma
dama ya gabata akan asuwaki, ana yi da
danye ko da busasshe, idan bai samuba
sai ayi da yatsa, amma mu sani asuwaki
daban kuskurar baki ma daban. Hakanan
kuma ko da mutum lokacin sallah ya yi
kuma amma yana da alwala to abinda ake
so shine ya yi asuwaki.
(5) Wuri Mai Tsarki: An so inda zaka yi
alwala ya zama wurine mai tsarki.
(6) Dama Kafin Hagu: abin nufi shine ka
fara wanke hannun dama kafin hannun
hagu, hakanan ka fara wanke kafar hagu
kafin ta dama.
( 7) Jerantawa: Wato jeranta kowacce
sunnah tare da 'yar-uwarta, kamar fara
gabatar da kuskurar baki kafin shaka
ruwa.
(8) Wankewa Sau Uku: Ma'ana wanke
wuraran da ake wankewa sau uku, mu
sani wankewa sau uku zai zama
mustahabbine idain wankewar farko ta
game ko ina, amma idan ta farko bata
gamaba to ta biyu tananan amatsayin
wajibi, haka namma idan ta biyun idan bat
agama ba to ta uku tana nan a matsayin
wajibi. Ya zama wajibi mai alwala mace ko
namiji ya kula sosai ya cuccuda inda ya
kamata ya sa ruwa ba tare da barnaba.
Amma shi kais au daya ake shafarsa, ba'a
shafar kai sau uku. Sannan kuma mutum
ya tabbata a wadannan wankewa da
akace ya yi sau uku bai kara akan hakan
ba, ya yi iya kokarinsa ya ga guda ukun
sun kammala.
Wadannan kadan kenan daga cikin
mustahabban alwala, kuma wadannan
bayanai sun mata kamar yadda suka shafi
maza, sai dai mata su sani gashin kansu
da sangalin hannuwansu duka al'aurane,
saboda haka bai halatta su bayyanar da su
ga maza, ken an idan zaki yi alwala sai ki
sami wuri ki kawwame kanki.
Wadannan bayanai da suka gabata zasu
haskaka mana yadda alwala take, amma
hanya mafi sauki shi ne a yi maka ita a
aikace ka gani domin haka sahabban
ma'aikin Allah suka yi, an tambayi Usman
dan Affan dan gane da alwala sai yasa aka
kawo mishi butar alawala ya yi musu ita a
aikace, yace kuma irinta ma'aikin Allah ce.
Anan nake kira ga dukkanin limamai na
juma'a dana sauran masallatai da kuma
malamai a jami'oi da kwalejin ilimi da
kuma malamai a sakandare da firamare
da malaman islamiyyu da malamai masu
karantarwa a masallatai da masu wa'azi
da sauran wadanda abin ya shafa da su
karantar da mutane ita wannan alwalar a
aikace kowa ya gani ya kuma yi tambaya,
kada ka ga kamar kowa ya gane da zarar
ka yi ta a aikace zaka ga abin mamaki, ni
na taba gwada hakan, ita ibada sai an
koyawa mutum ba wai daka kawai
shikenan ya iyaba, ko kuma ai shi iyaye da
kakanni duk musulmai ne sabo da haka ba
sai ya koyaba, duk wannan maganace ta
wanda yake nesa da makaranta, kai da
ganin alwalar wani kasan bai je
makaranta ba, Allah ya karba mana
ibadummu.
Kammalawa: Lalle wadannan bayanai
sun kara tabbatar mana ashe alwa abace
da sai an tashi tuku domin a koyeta tana
da falala da kuma sharudda sannan ga
farillai da sunnoni da kuma mustahabbai,
lalle ka nana bukatar malamai daga
kowanne bangare su tashi tsaye su
karantar da al'umma wannan ibada a
aikace, domin a gudu tare a tsira tare.
Comments
Post a Comment