AURE A MUSULUNCI

 ----AURE A MUSULUNCI----


     Aure shine hada wata irin alaka tsakanin mace da namiji , wannan yana nufin hade rayuwarsu su zama daya, haka nankuma makomarsu ta zama daya.

     Kowace irn al’umma akwai irin matsayin da ta bawa aure a musulunci wani dauri ne da yake halattawa ma’aurata  {mata Da miji} jin dadi a junansu ta hanyar saduwa da kuma sauran muamaloli

     ALLAH (SWT) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu (kamar yadda yagayamana a alkur’ani mai tsarki ). Wannan yana nun mana cewa alaka tsakanin mace da namiji ALLAH ne ya kulla tun fil’azal. Abin da ALLAH kuwa ya hada babu mai rabawa . wannan shine yasa a dabi’ance kowa ne namiji yana bukatar mace, haka kuma kowace mace tana bukatar namiji. Wato ko wane daya bazai iya wadatuwa dakansa ba, ya rayu shi kasai dole ne sai da wanin sa.

       ALLAH (SWT) da ya sanya wannan dangatakatsakanin mace da namiji bai barsu haka nan kara zubeba , suyi ta saduwa barkatai ba tare da wani tsari ba.saboda idan abin ya      zama haka tsarin rayuwar yan adam zai wargaje. Domin kuwa za ai ta samun “yaya barkatai batare da masu daukar nauyinsu ba. Don kuwa basu da wani uba guda daya tsayayye wanda zai dauki dawainiyarsu. Wannan zai sa rasa tausayi tsakanin alumma, domin kuwa babu wani wanda zai nuna cewa akwai wata alaka ta jinni tsakaninsa da wani wanda har zaisa ya rinka jin tausayinsa yana raga masa.

       Saboda haka ALLLAH ya hallata aure tsakanin mace da namiji, ya zama kuma cewa aure sunnace guda ta annabi ce da take wajibi a wajen duk mai iko   yayi shi. Kuma yazama dole kafin ayishi sai anyi sadaki da waliyai da kuma shaidu.

       Sadaki yana nufin ladan da zaa baiwa mace saboda halarta farjinta, kasancewar kuma mace bata aurar da kanta , ya zama dole asamu waliyi (mahaifinta ko danginta maza ko alkali ko sarki) da zai aurar da ita. Wannan zai iya zama garkuwa gareta daga wulakanici da zai iya yiwuwa mijinta yayi mata. Shaidu kuwa, domin su shaida kulla dangantaka aure tsakanin maauratan domin kiyaye da yin shaida kan dukan wani hakkoki da suka rataya da aure, zuriya da sauransu.  

Comments

  1. Shin idan an bada sadaki na kuma da shaidu da wiliyyai da wakilai yana halatta gareshi ya rike hannuna? Ina bukatar amsa cikin gaugawa don Allah domin gudun afkawa ga halaka..

    ReplyDelete
  2. Rabiu Ibrahim Chigari24 August 2015 at 10:10

    @miemie,
    ban fahimci tambayarkiba kiyimin bayani sosai.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA