RAYUWAR DUNIYA

DARASIN RAYUWA.

Wani Mutum Yana Cikin Motarsa Kirar Jeeb Sai Aka Tsayar Dashi Agurin Bayar Da Hannu Wato Traffic Sai Yaga Jirgin Sama Yazo Ya Gifta Sai Yake Rokon Allah Yasa Shima Ya Samu Kudi Yadinga Hawa Jirgi Daga Wani Gurin Zuwa Wani Gurin Don Yadinga Tsallake Cunkoso Da Tsaye-Tsaye Agurin Bayar Da Hannu.

*Daya Kalli Gefensa Sai Yaga Wani Mutum Cikin Wata Kwarababbiyar Mota Duk Tasha Jiki Tana Hayaki Gashi Duk Ta Ragwargwaje Yana Rokon Allah Inama Ace Yasamu Mota Kamar Ta Wannan Mutum Ba Ruwansa Da Wahalar Mota Da Zafin Cikin Motar.

*Shima Wanda Yake Cikin Motar Daya Kalli Gefensa Sai Yaga Wani Mutum Akan Dan Achaba Yana Rokon Allah Inama Ace Shine Yakeda Wannan Qaramar Motar Haka ? Idan Yanada Motar Kaga Ya Huta Da Zafin Ranar Nan Dayake Sha.

*Shima Nakan Dan Achaban Yana Waigawa Gefensa Sai Yaji Mutum Yana Addu'ar Allah Yabashi Kudin Da Zaike Hawa Dan Achaba Duk Inda Zaije Ya Huta Da Yawo Akafa Cikin Zafin Ranar Nan.

*Shima Yana Giftawa Kadan Sai Yaji Wani Gurgu Yana Addu'ar Inama Ace Allah Yabashi Kafafu Tayanda Zaike Tafiya Da Kafafunsa Kamar Yanda Kowa Ke Tafiya.

*Shima Gurgun Yana Gungurawa Gaba Kadan Sai Yaga Motar Asibiti Tazo Wucewa Dauke Da Wani Mara Lafiya Sunyi Hatsari Daya Daga Cikin Wanda Yayi Hatsarin Yana Rokowa Dan Uwansa Allah Inama Ace Ransa Allah Yabar Masa Ya Karbe Masa Kafafu Biyun Yakoma Gurgu.

DARASI
Duk Halin Da Ka Tsinci Kanka Aciki Ka Kasance Mai Godiya Ga Ubangijin Ka Allah.

Indai Wannan Darasin Ya Fadakar Dakai Ko Ya Fadakar Dake Mu Kasance Masu Yawan Ambaton
ALHAMDULILLAHI
ALHAMDULILLAHI
ALHAMDULILLAHI

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA