labari

YAN JAMIYYAR PDP SUN TADA YAMUTSI A WURIN TATTARA
SAKAMAKON A ABUJA..
Wakilin jam'iyyar PDP a zauren tattara sakamakon zabe
Najeriya, Elder Godsday Orubebe, ya kawo yamutsi a wajen
taron sanar da sakamakon zaben shugaban kasa a Abuja.
Yana mai cewa jam'iyyar PDP ba ta gamsu da rawar da
shugaban INEC, Attahiru Jega ke taka wa ba.
Jim kadan bayan bude zaman tattara sakamakon sai 'yan
PDP din suka tayarda hatsaniya.
Mr Orubebe ya ci karensa babu babbaka inda jami'an tsaro
sun ki cewa komai a kai.
Sai dai duk da batancin da ya rika yi a kan shugaban
hukumar INEC, Jega bai ce uffan ba.
Wakilan jam'iyyar APC sun yi masa magana amma ya rika
neman su da fada.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA