kyawun hali
KYAWUN HALI.
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
Ya Allah yi salati abisa wannan da ka aikoshi
domin ya zamo Rahama ga dukkan talikai baki
daya.
Ka sanya iyalan gidansa tsarkaka da
sahabbansa Madaukaka.
Yau zamu dan ce wani abu ne akan KYAWUN
HALI DA KYAUTATA HALAYE
Hakika shi kyawun hali shine mafi kyawun
Dabi'a. Kuma Shima aikin lada mafi daraja
awajen Allah (SWT).
Manzon Allah (saww) yana cewa:
"BABU WANI ABU MAFI NAUYI AKAN MIZANI
ARANAR ALKIYAMA FIYE DA KYAWUN HALI"
Harma yana cewa :
"NI FA AN AIKONI NE DOMIN IN CIKA
KYAWAWAN DABI'U"
Wato "MAKARIMUL AKHLAAQ".
Wadannan kyawawan halayen sun hada da:
HAKURI.
KYAUTA.
TAWADHU'U.
KUNYA.
JURIYA.
GASKIYA.
RIKON AMANA.
CIKA ALKAWARI.
KYAUTATAWA MAKOBCI.
AFUWA.
HADIYE FUSHI.
Wadannan da ma wasunsu, Duk Manzon Allah
(saww) ya hadesu. kuma yafi kowa cikar
wadannan halayen. Domin kuwa SHI Allah ne
da kansa ya tarbiyyantar dashi.
Shi yasa ma yake cewa:
UBANGIJINA SHINE YA TARBIYANTAR DANI.
KUMA YA KYAUTATA TARBIYYAH TA"
Dukkanin Annabawa (alaihimus salam)
kowannensu yana da wani hali guda 1 ko 2
wanda yayi fice akai.
Misali zamu ji Allah yana yabon Annabi Ayyub
(as) cewa Shi mai hakuri ne.
Hakanan Annabi Dawud da Annabi Sulayman
(alaihimas salam). Zakaji Allah yana siffantasu
da cewa Su masu Hukunci ne masu hikima
kuma masu Ilimi ne.
Hakanan Annabi Nuhu (as) Allah ya yabeshi da
cewa SHI BAWA NE MAI YAWAN GODIYA.
Hakanan Annabi Ibrahim (as) Allah ya bamu
Misalai da dama acikin Alkur'ani wadanda suke
nuna cewa Shi Annabi Ibraheem (as) mutum ne
mai yawan kyautatawa ga ba'ki.
Amma fa wadannan halayen gaba dayansu sai
Allah ya tattarasu ya bama Annabi
MUHAMMADU (SAWW).
Don haka Allah ya zabeshi ya zamto mafificin
halitta baki daya (saww).
Kuma Allah da kansa yake yabonsa yana ce
masa:
"HAQIQAH WALLAHI KAI KANA KAN WASU
DABI'O'I MASU GIRMA".
To hakanan kaima masoyinsa idan kana so ka
raya sunnarsa, to dole sai kayi koyi acikin
halayen nan nasa.
Ta haka ne kawai zaka tsere ma sa'anninka.
Ka samu darajoji awajen Ubamgijinka (SWT)
Alhamdulillahi anan zamu tsaya sai gobe kuma
insha Allahu.
Da fatan Allah si Qara mana son Manzon Allah
(saww) da kuma biyayya gareshi.
Ameeen.

Comments
Post a Comment