ALAJABI

LABARI MAI CIKE DA BAN AL'AJABI
Wannan labarin wani matashi ne dan kasar
Morocco amma
mazaunin kasar Amerika. Shi dai wannan
matashi ya
kasance faqiri ne bai mallaki wata dukiya da za
a iya nunawa ba.
Wata rana wata bukatarsa ta kai shi wani
kamfani mai irin dogon ginin nan a wani birni
daga cikin biranen kasar ta Amurka, sai ya
zamo cewa sai ya shiga lifter tukunna zai iya
isa ofishin da yake nema.
A lokacinda ya iso wurin
lifta sai aka yi rashin saá (ko kuma saá kenan
zan ce?) akwai mutane da yawa dake jiran
liftar, don
haka lifta na isowa suka dunguma gaba
dayansu suka shiga ta jasu tayi sama dasu.
Ana ta tafiya duk wanda aka zo hawan da yake
so sai ya sauka, har dai a karshe aka bar
wannan matashi daga shi sai wata kyakkyawar
yarinya
baturiya. A lokacin da wannan matashiyar ta
Ankara cewa yanzu fa daga ita sai wannan
matashin kawai suka
rage a cikin lifter, gashi kuma ta yi wata irin
mummunar shiga da ta tabbatar cewa babu
namijin da zai kalleta a cikin irin wannan
shigar face shaidan yayi kokarin ya saka masa
wani tunani sai kawai hankalinta ya tashi, tsoro
ya kamata, don bata san ko me zuciyar
wannan matashin ke saqa masa game da ita
ba yanzu. To
amma daga baya sai ta lura cewa wannan
bawan Allah shi ba mata ita yake yi ba, kuma
baya ma ko
kallon bangaren da take, kamar bai ma san da
ita ba. Ganin haka kuma kawai sai al'ajabi ya
kamata ta fara tunanin cewa wannan kuma
wanne irin mutum
ne haka da baya kallon mata,
musamman kasancewar ta yarda da kainta
sosai a wurin kyau. Tana cikin wannan tunanin
kawai
sai lifta ta tsaya ta bude, gogan
naka kawai sai ya sa kai ya fita da sauri ya nufi
inda zashi. Ai kawai yarinyar nan sai tayi wuf ta
sauko
ta biyoshi duk da cewa ita ba a nan zata sauka
ba, ta yi sauri
hade da gudu-gudu ta tari gabnsa tace masa
malam tsaya ina da Magana da kai. Bawan
Allah nan ya tsaya fuskarsa na kallon kasa
yace mata ina sauraronki. Budar bakin yarinyar
nan kawai
sai tace masa: Bani da kyau ne!?
Sai yace: Wallahi ban sani ba, don ban kalleki
ba. Sai tace: To me ya hana ka kalleni?
Me yasa baka yi kokarin yi mun
fyade ko cin zarafina ba? Sai yace: Aúzu
Billahi!! Ni kuwa
me zai kaini wannan danyen aiki bayan na san
Allah na kallona!?
Ina tsoron kada Allah Ya kamani. Sai tace: A
ina Allahn Yake harda kake jin tsoronsa haka?
Kafin ya bata amsa sai tace masa:
Yanzu kana nufin addininka ne ya hana ka
cutar dani duk da cewa daga ni sai kai, babu
wani mutum tare damu da zai iya hana ka
cutar dani? Sai yace: Hakane. Kawai sai
yarinyar nan taji cewa
ita kuma a duniya babu
mutuminda take kauna sai
wannan bawan Allah.
Sai ta kalleshi, shi kuma duk wannan zancen
da ake yi kansa na kasa be san ko da wa yake
Magana ba. Sai tace masa: Zaka iya aurena?
Sai yace mata: Menene addininki. Sai tace: Ni
ba musulma bace, bani
da addini. Sai yace: Ai baya halatta in aureki.
Sai tace: In na shiga addininka
zaka aureni? Sai yace: Eh mana, me zai hana?
Sai tace: Yaya zan yi in shiga
addininka?
Sai ya gaya mata Kalmar shahada, a take ta
karbi musulunci, aka daura musu aure bayan
yin duk abubuwanda musulunci ya tanada ga
irin wannan masálar. Sai bayan faruwar
wannan ne sannan wannan bawan Allah ya
fahimci cewa ashe wannan yarinyar wata
hamshakiyar mai
arziki ce mashahuriya a garin. Ita kuma daga
baya ta yanke
shawarar yin rijistar duk abinda ta mallaka
zuwa sunan wannan miji nata mai tsoron Allah,
don ta tabbatar da cewa tsoron Allah daya
hanashi ya cutar da ita a lokacin da suka
kadaiata daga shi sai ita a cikin lifta ba zai
taba barinsa ya cutar da ita ba tsawon
rayuwarta. Allah Yayi gaskiya: Da Yake
cewa“Kuma duk wanda yaji tsoron
Allah (to Allah) zai sanya masa
mafita kuma Ya azurtashi ta inda baya zato”
.Ubangiji Allah shi kara mana imani da jin
tsoronka a fili ko a boye.
Allahu Akhbar

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA