Alkwari Na four
ALKAWARI 4
Bayan nafice daga gidan ina cikin tafiya nafara tinani " to waye zai dauki wannan chek dinda na aje, bayan babu wanda yasan nayi ajiya agun?" wani bangaren na xuciyata kuma ya shaidamin "kadai koma kakara dubawa" banyi kasa a guiwa ba wurin juyawa, nadauki hanyarda zata kaini gida a saukake...
ina shiga nafara bincika ko ina acikin dakin, ina cikin dubawa ne naga wasu takaddu ajikin bango, dasauri nakarasa, abinda nagani shine yayi silar zubar hawayena batareda nasani ba, chek dinda yasmeen tabani ne amman saidai duk an ciccireshi da alama bera ne yaci rabonsa yabar sauran... Fitowa nayi daga gida nakoma bin gidajen mtane wa anda nasani ina fadamasu matsalata domin su taimakamin, atinanina zan iya hada kudin ta wannan hanyar, amman duk wanda natunkara da wannan maganar sai shima yanufoni da matsalar iyalinsa, haka nayini yawo acikin gari amman ba'asamu abinda ake nema ba...
magriba nayi nanufi asibiti bantsaya ko inaba sai wurin likita. Shiga nayi office din natarar akwai wasu mutane wa anda suke magana dashi. Wuri nasamu nazauna domin jiransu, jikina duk yayi sanyi hankalina atashe na hada kaina da guiwa inata tinani, muryar likitance ta doki dodon kunne na wanda hakan yayi silar maidoni daga duniyar tinanin da na afka. "inafatan dai ka hado kudinda za'ayi aikin gaba daya?" likita ne yake tambaya ta, nidai bance komai ba, saidai mikewa nayi tareda sanya hannu na acikin aljihu. Kudinda na fiddo shine yayi matukar ba likita mamaki wanda yasanyashi bude hangamemen bakinshi tareda fadar "kanada hankali kuwa?, amfada maka ana bukatar kudi naira dubu dari da ashirin, amman ka kawoman dubu biyu, me za'ayi da dubu biyu?"
yakarasa maganarsa wadda take kama da fada. Cikin wata sarkakkar murya nake fada, dan Allah kutaimaka kuyimata aikinnan wlh wa'annan kudin sune kadai ke garemu kuma bamuda kowa agarinnan dan Allah kutaimaka wlh zanbiya kudin koda bayan...
Tsaidani yayi da hannunsa, sannan yaci gaba da magana "wannan ka'idace ba'ayin aiki sai anbiya kudi duk irin tsananin ciwonda mutun ke fama dashi" ya ida maganarsa yana kallon fankar da keta faman juyawa makale saman office din domin bayarda iska. Ahaka natashi cikin kyarma nanufi hanyar fita waje, inazuwa bakin kofa naji muryar likitan yana fadar "daga gobe duk abinda yafaru da mahaifiyarka kada kazargi kowa kazargi kanka", kawai ficewa nayi ko juyowa banyiba, haka nanufi dakinda aka kwantarda umma, natarar da ita kwance duk an daureta da wasu karafa wanda suka tokare ko ina daga jikinta, batada damar da zata juya kanta balle tayi wani motsi, koda yaushe idanuwanta suna kallon sama, abinci kam saidai abata mai ruwa ruwa wanda zaya wuce batareda da taba hakoranta wahala ba. Inanan nida khadija har akayi kiran sallar isha'i, natashi nayi alwala nanufi masallaci nayi sallah sannan naroki Allah yafiddamu daga halinda muka tsinci kanmu...
Tafiya nike batareda nasan inda zanje ba, duk inda naga taron jama'a sai inje wurin infadamasu matsala ta domin sutaimakamin, cikin dan lokaci kankane nakoma kamar mahaukaci, hatta takalman dake sanye akafata sunyi spanner saboda tsabar tafiya kasa.

To oga ina labarin yasa gaba ne
ReplyDeleteyayi dadi sosai pls a cgb
ReplyDeleteAkawari full story
ReplyDeleteContinue oga
ReplyDeleteNice one guy
ReplyDeletedon allah kacigaba dawannan labari da number ka donbada shawara
ReplyDeletemungode dawannan labari munason acigaba pls
ReplyDelete