GANYEN NA'ANA'A

GANYEN NA'ANA'A

Na'a-na'a wani ganye ne mai kamshi mai yado wanda ke son guri mai dausayi sai ta yi ta yaduwa kafin wani dan laokaci duk guri ya cika

Na'a-na'a ganye ne mai matukar albarka yana da amfani sosai a wajen al'umma Larabawa da mutanen yankin Asiya sune mutanen da suka fi yin amfani da ganyen na'a-na'a a cikin abincinsu yawanci dukkan abincinsu zaka samu an saka na'a-na'a a ciki kodon ya karawa abincin kamshi ko don amfaninta a jiki hatta shayi in balarabe zai sha zaka tarar sau da dama sai ya hada da na'a-na'a a ciki

A bisa binciken da aka yi an gano cewa ganyaen na'a-na'a na da amfani sosai ga jikin dan adam musamman ma ga masu ciwon hauka in suka juri shan na'a-na'a koda yaushe zasu sami lafiya haka kuma ana amfani da shi wajen yin shayi magani kwalliya turare da sauransu

DAGA CIKIN AMAFANIN GANYEN NA'A-NA'A

1. Lizimtar amfani da ganyen na'a-na na maganin hauka

2. Shan ta nasa baki ya rinka kamshi koda yaushe sai yasa ake so wanda ya ci wani abu mai sanya warin baki kamar albasa ko tafarnuwa ya sha na'a-na'a bakinsa zai daina wari

3. Amfani da ita na hana fitowar kurajen fuska idan kuma ya riga ya fito sai a dimanci shafa man za samu dacewa musamman ga masu maikon fuska

4. Yin hayaki da busashshen na'a-na'a ayi turare da shi yana sanya kamshin jiki da kuma kanshi ga wurin da aka yi turaren haka kuma idan aka shaki kamshin da hayakin yana maganin mura

5. Shafa danyen ganyen aka na maganin ciwon kai haka kuma idan ana goge hakora da bushashshen shi yana sanya hakora su yi haske

6. Shan na'a-na'a da zuma na sanya karfin jiki kullum ka rika jin ka cikin nishadi da lafiyar hanta ta rika aiki da kyau da kawar da mura da narkar da abinci da karfafa zuciya ya zamanto cikin koshin lafiya koda yaushe da kuma kumburin ciki

7.Ga wanda yake fama da rashin jin dadi kamar wata matsala na damunshi idan aka yi shayinta ana shanta cikin kamshin ta da suga insha Allahu za a rabu da matsalar

8. Matsalar daukan ciki ga mata masu juna kamar masu yin amai ko yawan zubda yawu in sun samu ciki sai su samu ganyen su wanke suna taunawa ko kuma su sanya a bakinsu don ya dauke musu yawan zubda yawu amma su guji amfani da shi idan sun haihuwa domin yana rage ruwan mama

9. Ga matan da suke fama da ciwon ciki na al'ada in sun ji cikinsu ya fara ciwo sai su dafa ganyen suna sha

10. Wanda hancinsa ya toshe saboda mura ko majina sai a dafa ganyen bacin ya dahu sai a kifa kai akan ruwan ana shakar turirin

11. Ga wanda hadda ko karatu ke bashi wuya sai ya dafa ganyen ya abcin ya dahu sai ya hada da ruwan kahl fari dan kadan da zuma yana sha insha Allahu kwakwalwarsa zata bude ya rika fahimtar karatu cikin sauki

Comments

  1. Muhammad Iliyasu; daga garin "Wushishi", Niger state.1 December 2015 at 10:08

    Allah Ya Sakai Maka day alkhairi akan wannan muhimmiyar bayanai day kayi game da Magungunan da ganyen 'Na'a-Na'a keyi a jikin Dan Adam!! Ina mai matukar godiya!!!

    ReplyDelete
  2. Rabiu Ibrahim Chigari1 December 2015 at 10:51

    @Muhammad Iliyasu; daga garin "Wushishi", Niger state.,
    Yauwa Dan uwa mungode

    ReplyDelete
  3. ALLAH YA SAKA DA ALKHAIYRI. A TEMAKA MANA DA SUNAN SHI NA TURANCI KO KUMA NA KIMIYYA MANA, SABODA MU SAMU SAUKIN GANE SHI A INDA MUKE DA ZAMA.

    ReplyDelete
  4. Rabiu Yahaya chiromawa24 January 2016 at 10:18

    mallam, Ya Hayyu Ya Qayyumu Ya kara budi

    ReplyDelete
  5. SHA'AIBU DAN MALAMAWA6 August 2016 at 15:53

    ALLAH YA KARA MAKA KAIFIN KWAKWALWA AMEEN

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA