YAM CAKE

YAM CAKE

doya
nama
sugar
maggi
gishiri rabin cokali,
curry, thyme
kayan miya.

Dafarko xakisamu doyarki mai kyau guda daya. Kifereta
kiyanka daidai misali kizuba sugar babban cokali daya aciki
saiki daura a wuta.

Sannan kiwanke naman kisa thyme kiyanka albasa da maggi
guda daya kisa ruwan daidai yadda xaidafa naman harya
tsotse saiki kidaura bisa wuta har yadahu. Idan yadahu saki
nikashi kokuma kidakashi da attaruhu kamar biyu tattasai
daya kigoga albasa kixuba akan naman bayan kindaka kinsa
maggi kijuya yahadu kisoyashi kamar danbun nama amma
sama sama kamar minti goma, saiki yanka dafaffen kwai
kamar guda uku ko hudu akai.

Sannan kikoma kan doyarki data dahu kika sauke harma
tafara shan iska, kimurmusheta ko kidaka sama sama
kadadai tadaku sosai saimu xuba maggi da gishiri kisamu
prayn pan wanda baya kamu, kixuba mai kamar cokali biyu
ko uku.

Sannan kiraba dakakkiyar doyar xuwa gida hudu namanma
kiraba xuwa gida uku.saiki dauko doyar kashi daya kixuba
acikin kaskon kidauki naman kashi daya kixuba saman doyar
dama kuma kin kada kwanki agefe saiki xuba yalullube doyar
danaman saiki sake xuba doyar asaman kwan kisake xuba
naman dakwan har kaskon yakusa cika saiki xuba kwan
dayawa yadda xai lullubesu gabadaya kidora awuta ammafa
karkibashi wuta sosai kibarshi kamar minti 20/30 kisamu
murfin tukunya wanda xairufe kaskon kirufe yadda kwan
sama xai dahu. Idan yagama saiki samu faranti mekyau ki
kwakkwafe a hankali xakiga yafita kamar cake saikisa wuka
kiyanka yadda kikeso, kuma kina iya gasawa a oven.
Aci dadi lafia!

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA