Wata Sabuwa! Matan Nijeriya Ne Mafi Iya Yaudara A Duniya

Sakamakon wani binciken musamman da aka gudanar, an gano cewa matan kasar Nijeriya su ne a layin farko na matan da ke cin amanar maza a doron duniya.
An samo wannan rahoton ne daga wani gidan talbijin a kasar Indiya mai suna, INDIAN TbNEWS, inda ya nuna cewa matan da suka fi yin fice a bangaren cin amanar aure, gami da yaudarar maza su ne wadanda suka fito daga wadansu kasashe guda takwas, inda Nijeriya ta kasance ta farko a rukunin.
Mashahurin kamfanin nan mai sarrafa koron-roba, wato ‘Condom,’ DURED LTD. ne ya gudanar da binciken. Inda ya bayyana cewa, kafin hada alkaluman, sai da suka tattaunawa da kimamin mutane dubu ashirin da tara a kasashe daban-daban har 36 na duniya, sannan uka bi kadin al’amuran da ke faruwa a cikin kasashen, bayan nan ne aka bayyana sakamako.
Ga yadda alkaluman binciken nasu ya tabbatar:
Nijeriya: Kashi 62 cikin 100 na matan Nijeriya suna yaudarar mazajensu.
Thailan: Ita ce kasa ta biyu, inda binciken ya tabbatar kashi 59 cikin 100 na matan suke yaudarar mazajensu.
Ingila: A kasar Birtaniya kusa, binciken ya nuna kashi 42 ne cikin 100 suke da wannan matsalar
Maleshiya: Kashi 33 cikin 100 na matan Maleshiya suna da matsala wajen rike amanar aurensu.
Rasha: Ita ma kasar Rasha ta yi kunnen-doki da Maleshiya wajen cin amanar aure, inda akalla ta samu kashi 33 cikin 100.
Singapo: Kamfanin na Dured ya sanar cewa kimamin kashi 19 cikin 100 na matan Singapor suna da matsala da mazajensu.
Faransa: A kasar Faransa kuwa, kusan kashi 17 ne cikin 100 na gurbatattun mata masu yaudarar mazajen nasu.
Amurka: An bayyana cewa Amurka ce kasa ta takwas na mata masu yaudarar maza a duniya. Binciken ya tabbatar cewa kashi 14 ne cikin 100 na mata masu tsananin yaudarar mazajensu a kasar.

Comments
Post a Comment