WASIYYAN UBA CIKIN HIKIMA.

WASIYYAN UBA CIKIN HIKIMA.

Wani mutum ne yana bisa gadon asibiti yazo gangaran mutuwa sai yacewa dansa,"yaa dana naso nayi maka wasu nasihu guda hudu,amma bazan samu yi maka su yanzu ba sbd nasan mutuwa zanyi,abinda nakeso da kai idan na mutu kaje wajen TSOHON DOKI da KARE da KIYASHI da MESA(maciji) kafada musu na aiko ka suyi maka nasiha za suyi fada abinda nakeso na fada maka.

Yana gama fadawa dan nasa haka ya cika da karman shada.

Dan yai kuka sosai, bayan anyi sadakan uku sai dan ya tashi ya tafi wajen TSOHON DOKI yace"babane kafin ya mutu yace idan ya mutu nazo wajenka da KARE da KIYASHI da MESA wai zakumin nasiha.

Tsohon doki yace,"lallai mahaifinka yayi gaskiya,abinda yakeso ya fada maka wanda yace kazo na fada maka shine,duk abinda zakayi kayishi cikin kuriciyarka kayishi akan lokaci kada ka bari lokaci ya kure maka bakai ba,kaganni lokacin ina saurayi da karfina ana kawomin abinci akan kari,ana min wanka kullum, ana sharemin wajen kwanciyana, ammayanzu dana tsufa dubi inda nake kwanciya kuma har yanxu va'a kawomin abinci va,to wannan shine nasihar da mahaifinka keso yai maka.

Yaro yai godiya ga tsohon doki ya kama hanya ya nufi wajen KARE ya fadawa kare kamar yadda ya fadawa TSOHON DOKI.

KARE yacewa yaron,"to zo muje",yaro yabi kare,kare yaja yaro zuwa wata makarantar almajirai,ai kuwa almajirai na ganin kare suka bishi da jifa kare da yaron suka taka da gudu dakyar kare yasha,daganan kare bai zame ko ina ba sai gidan wani mafarauci,suna zuwa mafarauci ya kama kare yamai wanka ya kawo masa abinci da nama,kare yaci, bayan ya gama ci sai yacewa yaron,"to abinda ubanka keso yafada maka anan shine duk abinda zakayi kayishi tare da masoyinka kada kayi da makiyinka,kaga da mukaje makarantan almajiran can biyoni sukayi sbd ba masoyana ba,amma da muka zo wajen wannan mafaraucin kaga yada ya alkintani ya vani abinci da nama da ruwa,sbd shi masoyina ne,to wannan itace nasihar mahaifinka bissalam".

Daga wajen kare yaro ya wuce wajen KIYASHI ya fada masa duk abin mahaifinsa ya fadamai.

Shima kiyashi yacewa yaron tashi "muje na gwada maka abinda mahaifinka keson fada maka",yaro ya tashi yabi kiyashi suna cikin tafiya sai suka ci karo da mushen kyankyaso kiyashi yacewa yaron jirani anan,ya tafi gida ya kira yan uwansa suka zo suka tayashi daukar kyankyaso su kai gida.

Duk yaron na kallo,can jimawa kiyashi ya dawo yace,"mahaifinka naso ya fada maka duk abinda zakayi kada kayi kai kadai kayi da yan uwanka ko ka nemi shawarar su a hakane zakaji dadin zaman duniya".

Yaro ya kada kai ya tafi neman MESA dakyar ya sameta a wani kogon dutse,ya kwashe duk abinda ke tafe dashi ya fadawa macijiyar.

Sai mesa taja gwaron numfashi ta aje sannan tace"mahafinka naso yayi maka nasiha akan ka iya bakinka kada ka vari vakin ka ya kaika ga halaka,ka ganninan bana fita ko ina sai cikin dare,sbd inna fita aka ganni kasheni za'ayi bakomai yajamin ba illa bakina,wannan itace wasiyar mahaifinka".

*
Ba sai nayi karin bayani akan wannan lbr ba sbd wasun ku sunsan lbrn wadanda basu sani ba kuma sun gane me akeso su gane game da lbrn.

Comments

Popular posts from this blog

SUNAYEN SAHABBAN ANNABI (S.A.W) GUDA GOMA WA "YANDA SUKA MUTU DA CERTIFICATE NA SHIGA ALJANNAH

FARILLAN SALLAH

MTN BONANZA