WACCE ZA KA AURA A CIKI?
WACCE ZA KA AURA A CIKI?
Al’anaanah: Mace mai jinini da tsirtiya a kodayaushe,
wadda kullum a shirye take ta kai karar miji ko saurayi,
sannan ba ta da sirri ko na sisin kwabo.
Al-manaanah: Mai yawan shimfida hannuwanta
wajen bayar da kyauta ko alheri, amma idan abu ya
faru a gaba, sai ta yi wa mijinta gorin cewa ta yi kaza da
kaza domin shi.
Al-hannanah: Mace mai tuna baya kan tsohon mijinta
ko saurayinta, har ta rika cewa ai da wane ne, da ba zai
yi mata haka ba. Ko kuma ta rika sambatu da sunan
wani alhali tana tare da kai
Al-Kannaanaa: Mace mai yawan surutu tare da
alfahari da dukiyar iyayenta ko ‘yan’uwanta,
musamman sarautar mahaifinta da sauransu.
Al-hadaakah: Mai zuba idanu kan abin duniya. Komai
ta gani sai ta nuna maita da kwadayinta a fili, ba ta iya
boye abin take so, sannan za ta iya takurawa ta matsa
lamba, ba za ta kwantar da hankalinta ba, har sai an
saya mata, ta kowane hali.
Al-barrakah: Mai yawan bata lokacinta wajen gyaran
fuska domin birge maza, kuma ba ta damu da zubar da
kimarta gaban ko waye ba. Za ta yi kwalliya ba don
mijinta kawai ba, sai domin a ce ta yi kyau, ko kuma
kawaye, ‘yan’uwa da abokan arziki su ce tana jin dadi a
dakin mijinta.
Al-sadakah: Mai zubar gadon kalamai, wadda ba ta
da linzami ko miskala zarratin ga harshenta.

Comments
Post a Comment